Kisan Basarake Ya Tayar da Tarzoma, An Kashe Mutane Fiye da 60 a Matsayin Ramuwar Gayya

Kisan Basarake Ya Tayar da Tarzoma, An Kashe Mutane Fiye da 60 a Matsayin Ramuwar Gayya

  • Akalla mutane 64 ne aka ruwaito sun mutu a harin ramuwar gayya da wasu da ake zargin ’yan sa-kai ne suka kai a Wawa da Gada Oli, Jihar Neja
  • An kai harin ne bayan wasu ’yan bindiga sun kashe dagacin Lumman-Ba’are, matarsa da ’ya’yansa uku
  • Shugaban MACBAN a Neja ya ce an birne mutum 64, yayin da wani jagoran al’umma ya tabbatar da birne mutum 38 a Wawa kaɗai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Akalla mutane 64 ne aka ruwaito sun mutu a wani harin ramuwar gayya da wasu da ake zargin ’yan sa-kai ne suka kai kan Fulani a Wawa da Gada Oli, da ke Karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.

Bayani sun nuna cewa harin ramuwar gayyar, wanda ya faru ranar Asabar, ya biyo bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai da sanyin safiyar ranar a ƙauyen Lumman-Ba’are.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yan bindiga sun rutsa sarki da wasu bayin Allah suna cikin Sallah

Niger.
Taswirar jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta rahoto cewa a yayin harin, an kashe dagacin ƙauyen, Malam Bawa Muhammad, matarsa da kuma ’ya’yansa uku.

Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen Jihar Neja, Ardo Umar Lapai, ya ce an kashe Fulani 64 a hare-haren ramuwar gayya da aka kai Wawa da Gada Oli tsakanin ranar Asabar da Lahadi.

Ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta shiga tsakani domin magance matsalar tsaro a ƙananan hukumomin Borgu da Agwara.

Ya kuma yi zargin cewa al’ummomin Fulani da ke yankunan da abin ya shafa sun sha fama da satar shanu, garkuwa da mutane da sauran hare-hare, inda ya ce lamarin na buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa da ƙuduri.

Yadda harin ramuwar gayyar ya faru

Jagoran al’ummar Wawa ya bayyna cewa harin ramuwar gayya da aka kai kan matsugunan Fulani a garin Wawa da Gada Oli ya biyo bayan bayanan da ake zargin wani ɗan bindiga da aka kama ne ya bayar bayan harin Lumman-Ba’are.

Kara karanta wannan

2027: Magoya bayan APC sun yi takansu da rigima ta ɓarke a wurin yakin neman zaben gwamna

Ya ce an kashe ɗaya daga cikin maharan yayin musayar wuta da ’yan sa-kai, yayin da aka kama wani da ransa bayan ya samu raunin harbin bindiga, amma daga baya ya mutu.

A cewarsa, ’yan sa-kan sun yi zargin cewa lokacin da suke yi wa wanda aka kama tambayoyi, ya gaya musu cewa maharan sun fito ne daga Gada Oli, mai nisan kusan kilomita 70, domin kai hari Lumman-Ba’are.

Jagoran ya ce:

“Abin da ya jawo harin ramuwar gayyar shi ne, yayin musayar wuta da ’yan bindiga, an kashe ɗaya, aka kama wani da ransa bayan ya samu raunin harbin bindiga.
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda aka kama ya bayyana cewa daga Gada Oli suka fito, mai nisan kusan kilomita 70, domin kai hari Lumman-Ba’are.
“Saboda haka, ’yan sa-kan sun tara mutane da yawa suka nufi Gada Oli domin ‘share’ al’ummar gaba daya.

Ya ce a kan hanyarsu ta zuwa Gada Oli, sun riƙa harbin mutanen da suka ci karo da su har suka isa. Kasancewar kauyen Wawa yana hanyar da ta tashi daga Lumman-Ba’are zuwa Gada Oli, ’yan sa-kan sun tsaya a garin su ma sun kashe mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262