Tinubu Ya Zabi Manyan Hadiminsa da Gwamnoni 5, Ya Shirya Masu Liyafa a Makkah

Tinubu Ya Zabi Manyan Hadiminsa da Gwamnoni 5, Ya Shirya Masu Liyafa a Makkah

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya shirya liyafa ga wasu shugabanni, attajirai da hadimansa a birnin Makkah
  • Shugaban Najeriya ya ci abinci tare da gwamnoni irinsu Malam Uba Sani da Farfesa Babagana Umara Zulum
  • 'Yan kasuwa, Abdussamad Rabiu da Wale Tinubu suna cikin wadanda aka gani a tawagar shugaban kasar a Saudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yana ƙasa mai tsarki inda ya yi ibadar Umrah bayan barin gida a makon jiya.

Da yake Saudi, Bola Tinubu ya roƙi Allah SWT ya mayar da bambancin da ke tsakanin al’ummar Najeriya ya zama alheri.

Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da wasu manyan Najeriya a Makkah Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Addu'ar Shugaba Bola Tinubu a birnin Makkah

Daily Trust ta ce shugaban ƙasar ya roka wa Najeriya arziƙi, haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa domin amfanin jama’a.

Tinubu ya yi wannan addu’a ne a ranar Lahadi a birnin Makka da ke ƙasar Saudiyya, yayin da yake karɓar baƙuncin wasu manya.

Kara karanta wannan

"Dogaro ga Allah SWT da wasu abubuwa 2 da za su taimaki Shugaba Tinubu a zaɓen 2027"

Mai girma Shugaban Najeriyan ya shirya wa wasu ‘yan tawagarsa a liyafar cin abinci ta musamman a birnin Makkah a ƙasar Larabawa.

Hadimin Bola Tinubu ya fitar da jawabi

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkoki da dabarun yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar da cikakken bayani a shafin Facebook.

A cikin sanarwar, Cif Onanuga ya ruwaito shugaba Tinubu ya ce yana fatan bambancin ƙabila, addini da al’adu su zama ƙarfi ba rauni ba.

Ya yi fatan su zama abin ƙarfafa haɗin kai da ci gaban ƙasa, maimakon zama sanadin rarrabuwar kawuna al’umma a Najeriya.

Onanuga ya ce Shugaban ƙasar ya roƙi Allah da ya azurta Najeriya da zaman lafiya mai ɗorewa, kwanciyar hankali da wadata.

Ya kuma roƙa wa Najeriya shugabanni masu hikima da jajircewa domin jagorantar ƙasar ta yadda za su inganta rayuwar jama’a.

Waɗanda suka halarci liyafar da aka yi

A mahalarta liyafar akwai gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani; gwamnan Jigawa, Umar Namadi.

Haka kuma an ga gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu; da gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum tare da shugaban ƙasar a Makkah.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi Umrah a Saudiyya, ya bayyana addu'o'in da ya yi wa Najeriya

Sauran waɗanda suka halarci cin abincin sun haɗa da Ministan Lafiya da Walwalar Al'umma wato Farfesa Mohammed Ali Pate.

Sannan akwai Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu; Babban Daraktan Kamfanin Oando Plc, Wale Tinubu.

Sai mai Bai Shugaban Ƙasa Shawarar Siyasa, Ibrahim Masari; da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Addu'ar da gwamnan Kwara ya yi wa Tinubu

Gwamnan Kwara kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), ya ce suna matuƙar jin daɗin ƙoƙarin da Tinubu yake yi.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya roƙi Allah ya ƙara wa Tinubu ƙarfin guiwa tare da ba shi hikima domin jagorantar Najeriya.

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, SAN, shi ma ya yi addu'a ga Shugaban ƙasar.

Ya roƙi Allah SWT ya ci gaba da ƙarfafa Tinubu wajen tabbatar da shugabanci nagari da adalci ga dukkan 'yan Najeriya.

Abin da Abdulsamad Rabiu ya fada wa Tinubu

Da yake jawabi a wurin liyafar, shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Isiaka Rabiu, ya sake tabbatar da goyon bayansa.

Kara karanta wannan

'Ba dalilin zaɓenka ba kenan': Ƴan Najeriya sun fusata da Tinubu ya je Makka addu'a

Abdussamad Rabiu ya ce sun tattauna muhimmancin ci gaba da yi wa Najeriya addu'ar samun zaman lafiya da haɗin kai.

Ya ce za su ci gaba da tallafa wa Tinubu ta kowace hanya da za su iya, yana cewa shugaban ƙasar yana matuƙar ƙoƙari a mulkinsa.

Abdussamad Rabiu ya ci riba da siminti

An samu rahoto cewa kamfanin simintin BUA Cement ya samu ribar Naira biliyan 463.1 cikin watanni kuma fiye da N1.09tr ya shigo masa.

Attjirin wanda shi ne na biyu duk fadin Najeriya ya samu sama da Naira biliyan 180 daga rabon ribar da aka biya masu hannun jari da aka yi.

Abdul Samad Rabiu mutumin Kano mai shekaru 66, shi ne wanda ya kafa kuma shugaban rukunin kamfanonin BUA Group na duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng