Da Gaske An Daure Mace Kirista saboda Ta Sa Musulmi Ya Yi Ridda? An Samu Bayani

Da Gaske An Daure Mace Kirista saboda Ta Sa Musulmi Ya Yi Ridda? An Samu Bayani

  • Kungiyar PFN da CLASFON sun bukaci Kiristoci su guji gaggawar yanke hukunci kan hukuncin da aka yanke wa Lami Samuel Dawa a Borno
  • An yanke wa Lami, wacce kirista ce hukuncin zaman gidan yari na shekaru 14 a wata babbar kotun jihar Borno
  • CLASFON ta bayyana cewa tuhume-tuhumen sun hada da sace yaro da fitar da shi daga hannun iyayensa, ba wa’azi kadai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Najeriya – Manyan kungiyoyin Kiristoci sun bukaci ’yan Najeriya da su yi taka-tsantsan tare da kauce wa yada bayanan da ba a tantance ba game da hukuncin da aka yanke wa wata kirista, Lami Samuel Dawa a jihar Borno.

Kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) da Christian Lawyers Fellowship of Nigeria (CLASFON) ne suka yi wannan kira a daidai lokacin da lamarin ke jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Lami Dawa.
Lami Samuel Dawa, matar da aka yanke wa hukunci kan safarar yara a Borno Hoto: @Dipoaina01
Source: UGC

Jaridar Leadership ta rahoto cewa an yanke wa matar hukuncin dauri a gidan yari na tsawon shekaru 14 a jihar Borno kan laifin da ya shafi raba wani yaro da iyayensa.

Lamarin da jawo cece kuce, inda wasu Kiristoci ke bayyana daurin Lami Dawa a matsayin nuna wariya ga addininsu.

PFN ta gargadi masu gaggawar hukunci

Sakatare Janar na PFN, Bishop David Bakare, ya shaida wa The Punch cewa kungiyar ta gudanar da bincike kan lamarin, kuma ta gano cewa bayanan da ake yadawa a bainar jama’a ba su da alaka da hakikanin yadda shari’ar ta kasance.

Bakare ya ce:

“An sanar da PFN game da shari’ar, amma bincikenmu ya nuna cewa lamarin ba haka yake ba kamar yadda ake yadawa a bainar jama’a.
"Ina shawartar masu magana kan shari’ar da su gudanar da cikakken bincike. Muna taka-tsantsan, ba ma son mu shiga shari’a kawai ba tare da sanin hakikanin abin da ya faru ba. Ba ma son a rika yi mana kallon mutanen da ba su da masaniya.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna da suka farmaki dakarun sojoji a Plateau

Ya kara da cewa kungiyar ta gamsu da cewa an riga an daukaka kara kan hukuncin.

CLASFON ta bayyana tuhume-tuhumen

Ephraim Yidawi, shugaban reshen CLASFON na Maiduguri, ya ce kungiyar ta wakilci Lami Dawa da wasu mutum hudu da ake tuhuma tare da ita a lokacin shari’ar.

Yayin da aka samu Lami Dawa da laifi, kotun ta sallami sauran mutum hudun tare da wanke su.

Yidawi ya yi gargadin cewa bayyana shari’ar a matsayin batun wa’azi ko sauya addini kadai ba daidai ba ne.

Ya ce tuhume-tuhumen sun hada da hada baki wajen sace yaro, yaudarar yaro ko lallashinsa ya bar hannun iyayensa, fitar da yaro daga kulawar iyayensa ta doka, hana shi samun ilimi da kuma tsoma baki a harkokin addininsa da sauya addininsa.

Ya tabbatar da cewa an daukaka kara kan hukuncin, kuma tawagar lauyoyin na bin matakan shari’a da suka dace.

Borno.
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Lauya ya yi tsokaci kan shari’ar

Legit Hausa ta tattaro Muhammed Adam Ndakudu, wani lauya dan Najeriya da ya shahara a dandalin X, shi ma ya yi tsokaci kan lamarin.

Kara karanta wannan

Jerin labaran karya da suke yawo a yanar gizo da za a iya dauka gaskiya ne

Luyan ya ce ya karanta cikakken hukuncin kotun kuma ya gargadi wani mai amfani da X da ya yi ikirarin cewa an daure LaminDawa ne saboda “ta sa wani musulmi ya koma kirista."

Ndakudu ya rubuta cewa:

“Wadannan su ne batutuwan da ake magana a kai. Mutane suna neman batutuwan da suka yi fice ne domin shafukansu su samu mabiyanta hanyar yada bayanan karya da masu yaudarar jama’a.
"Ba ka karanta hukuncin kotun ba. Ba ka gudanar da wani bincike na kanka ko tantance bayanai ba. Ya kamata ku gyara halayenku, ku daina haddasa tashin hankali marar amfani a kasar nan.”

Mata ta kona diyar mijinta a Borno

Kun ji cewa an kwantar da wata mai shayarwa, Zara Muhammad, a asibiti bayan zargin cewa matar mahaifinta ta kona ta da ruwan zafi a yankin Kofa da ke Maiduguri, Jihar Borno.

Shaidu sun ce rikicin ya samo asali ne daga gardama tsakanin matan biyu, kafin lamarin ya rikide zuwa mummunan hari da ya jikkata Zara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262