"Atiku Abubakar Zai Lashe Jihohin Arewa 13 a Zaben Shugaban Kasa na 2027"
- Mataimakin dan takarar shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar zai lashe jihohi 13 a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma
- Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce ADC za ta kuma lashe jihohin Neja, Kogi da Nasarawa a Arewa ta Tsakiya
- Ya yi alkawarin cewa gwamnatin Atiku za ta dawo da tallafin man fetur, yaki da cin hanci da rashawa tare da magance matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Nigeria - Mataimakin dan takarar shugaban kasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa Atiku Abubakar, zai samu nasara a jihohi 13 na yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma a zaben shekarar 2027.
Amaechi ya kuma yi hasashen cewa ADC za ta lashe jihohin Neja, Kogi da Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiya, yayin da ya dage cewa Shugaba Bola Tinubu zai sha wahala wajen samun kuri’u a wasu yankunan kasar.

Source: Twitter
Leadership ta ce ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na ADC a Bauchi, inda ya nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta iya kayar da APC mai mulki a zaben 2027.
A cewar tsohon gwamnan Jihar Rivers, Atiku zai lashe dukkan jihohi shida na Arewa maso Gabas da kuma jihohi bakwai na Arewa maso Yamma, wanda hakan zai ba ADC damar samun nasara a jihohi 13 na yankunan biyu.
Sai dai ya yi ikirarin cewa Tinubu zai samu nasara ne a jihohi biyar kacal na Kudu maso Yamma, yayin da jam’iyyar APM za ta lashe jiha ta shida.
Amaechi ya kara da cewa ADC za ta fafata da APC a yankunan Kudu maso Kudu da Arewa ta Tsakiya, inda ya nuna kwarin gwiwar cewa Atiku zai lashe jihohin Neja, Kogi da Nasarawa cikin sauki.
Ya ce:
"Ku tabbatar da cewa jihohin Neja, Kogi da Nasarawa za su kasance a hannunmu cikin sauki. Ko ba haka ba? Ba zai samu nasara ko kadan a Kudu maso Gabas ba. Ku kwantar da hankalinku, za mu yi nasara.”
Amaechi ya kuma bayyana wasu daga cikin muhimman tsare-tsaren tattalin arziki da tsaro na ADC, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatin da Atiku zai jagoranta za ta dawo da tallafin man fetur domin rage tsadar rayuwa.
Ya ce jam’iyyar ta fahimci matsalolin tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta, kuma za ta bullo da tsare-tsaren rage kudin sufuri, inganta damar gudanar da harkokin noma da kuma magance matsalar rashin tsaro.
Ya ce ADC a shirye take ta sauya alkiblar siyasa da tattalin arzikin kasar idan aka zabe ta a shekarar 2027, inda ya nuna kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta samu nasara.
Amaechi ya kafa sharadin yin murabus
Kun ji cewa Rotimi Amaechi ya ce zai iya yin murabus daga muƙamin mataimakin shugaban ƙasa a gwamnatin Atiku Abubakar.
Amaechi ya ce a shirye yake ya yi murabus idan gwamnatin Atiku Abubakar ta gaza gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Asali: Legit.ng

