Tinubu Ya Shiga Rikicin Ibrahim Masari, Gwamna Radda da 'Yan APC, Ya Bayar da Umarni

Tinubu Ya Shiga Rikicin Ibrahim Masari, Gwamna Radda da 'Yan APC, Ya Bayar da Umarni

  • Tinubu ya umarci mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, da ya sasanta ’yan APC da ke fushi da juna, musamman a jiharsa ta Katsina
  • Shugaban ƙasar ya ce Masari ya fara aikin sulhu a Katsina, sannan ya wuce Jigawa da sauran sassan Najeriya domin dawo da haɗin kan jam’iyyar
  • Umarnin ya zo ne bayan murabus ɗin wasu jami’an gwamnatin Katsina a watan Oktoba 2026, a lokacin da ake zargin rikicin siyasa tsakanin Masari da Gwamna Dikko Radda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, da ya fara aikin sulhunta ’yan jam’iyyar APC da ke cikin saɓani da juna.

Tinubu ya ce Masari zai fara aikin ne daga jiharsa ta Katsina, kafin ya wuce jihar Jigawa da sauran sassan Najeriya domin sasanta waɗanda ke da ƙorafe-ƙorafe a cikin jam’iyyar.

TheCable ta ce shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne yayin wani taron APC da aka gudanar a Legas ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba, inda ya bayyana Masari a matsayin amintaccen mutum kuma jagoran siyasa mai ƙarfi.

Wane umarni Tinubu ya ba Ibrahim Masari?

Tinubu ya buƙaci Masari da ya tuntubi dukkan waɗanda ke jin haushi ko suka nuna rashin gamsuwa da wasu abubuwa a cikin jam’iyyar.

Ya ce wajibi ne a nemi afuwar waɗanda aka ɓata wa rai, domin dawo da haɗin kai da zaman lafiya tsakanin mambobin APC.

A kalamansa, shugaban ƙasar ya ce:

“Ga amintaccena kuma gwarzon siyasa, Alhaji Masari, ka koma gida ka sasanta da kowa. Wannan umarnin shugaban ƙasa ne. Idan ka gama, ka wuce Jigawa da sauran wurare, ka sasanta su, ka nemi afuwarsu.

“Badaru, ka fahimci abin da na faɗa? Dole ne mu sasanta. Dole ne duk wani fushi ya ƙare.”

Murabus ɗin jami’an gwamnatin Katsina

Umarnin Tinubu ya zo ne bayan jerin murabus ɗin wasu naɗaɗɗun jami’an gwamnatin jihar Katsina a watan Oktoba 2026.

Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa aƙalla jami’an siyasa biyar ne suka ajiye mukamansu cikin ’yan kwanaki.

Daga cikinsu akwai mataimakin kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Katsina mai kula da ayyuka, Muhammad Shitu Maslaha, wanda ya sanar da murabus dinsa kwana guda bayan kwamandan hukumar, Dakta Aminu Usman, wanda aka fi sani da Abu Ammar, ya ajiye nasa mukamin a ranar 5 ga Oktoba, 2026.

Sauran sun haɗa da shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar, Alhaji Bature Sarkin Alhazai; babbar mataimakiya ta musamman ga gwamna kan aiwatar da ayyuka, sa ido da tantancewa, Fadila Sani Dalhatu; da mai ba gwamna shawara kan bunƙasa matasa, Alhaji Abubakar Soja Tsanni.

Ana zargin saɓanin siyasa tsakanin Masari da Radda

Ko da yake waɗanda suka yi murabus ɗin ba su bayyana cewa sun ɗauki matakin ne saboda saɓanin siyasa tsakanin Masari da Gwamna Dikko Umaru Radda ba, mutane da dama sun danganta lamarin da rikicin.

An sha zargin Masari da amfani da matsayinsa a fadar shugaban ƙasa wajen tsoma baki a harkokin siyasar Katsina.

Rahotanni sun kuma nuna cewa Gwamna Radda ya nuna damuwa kan yadda ake zargin wasu daga Abuja na shiga harkokin siyasar jihar.

Sai dai Masari ya sha musanta cewa akwai wata matsala tsakaninsa da gwamnan.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa a baya-bayan nan, Masari ya yi watsi da zargin cewa suna rikici da Radda, yana mai cewa babu abin da ya yi wa gwamnan face alheri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng