2027: Kwankwaso Ya Yi Maganar Makomar Tallafin Fetur a Gwamnatin Peter Obi
- Rabiu Kwankwaso ya ce jam’iyyar NDC na iya dawo da tallafin man fetur idan ta lashe zaɓen shugaban kasa
- Ya ce cire tallafin ya jefa ’yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki, kuma har yanzu ba su gama farfadowa ba
- Idan sun shiga ofis, ya nuna jam’iyyarsu za ta dauki matakan da suka dace domin su saukaka wa ’yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso mai takarar mataimakin shugaban kasa a NDC ya yi zancen yiwuwar maido tallafin fetur.
'Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya ce jam’iyyar za ta dauki duk matakan da suka dace domin a rage farashin mai.

Source: UGC
An yi hira da Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso ya yi maganar dawo da tallafin man fetur idan jam’iyyar ta lashe zabe ne a hirar shi da Channels.
A ranar Alhamis aka yi wata hira da aka yi da shi a shirin siyasa na Politics Today domin jin inda jam’iyyarsu ta sa gaba.
Tattanawar ta tabo zancen alakarsa da Atiku Abubakar, hadaka, siyasa da sauran sha'anin mulki.
Ana cikin radadin janye tallafin man fetur
A ranar 29 ga Mayun 2023 ne Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a lokacin rantsar da shi kan mulki.
Tun bayan nan litar fetur ya yi ta tashi daga kimanin N200 zuwa kusan N1, 500 a halin yanzu.
Rabiu Kwankwaso ya ce har yanzu ’yan Najeriya ba su farfado daga matsin tattalin arzikin da cire tallafin man ya haifar ba.
Kamar Peter Obi, ya nuna yaki da cin hanci da rashawa a bangaren man fetur na iya taimakawa wajen magance wannan matsala.
Ya ce:
“Mun ga illar cire tallafin tun daga ranar farko har zuwa yau. Ina ganin har yanzu babu wanda ya farfado daga girgizar tattalin arzikin da cire tallafin ya haifar.”
Matsayar NDC a kan tallafin man fetur
Tsohon gwamnan ya ce shugabannin NDC sun sha zama domin tattauna matsalolin kasar da yadda za a magance su idan an ci zabe.
Sun kuma duba abubuwan da suka faru a lokacin Peter Obi a Anambra da nasa mulkin a Kano, tare da na jagoransu, Seriake Dickson.
The Cable ta bibiyi hirar, ta rahoto Kwankwaso ya ce jam’iyyar za ta yi duk abin da za ta iya domin saukaka wa talakawa rayuwa.
Madugun na Kwankwasiyya ya kara da cewa halin rayuwa a Najeriya ya yi tsanani matuka.
'Dan takaran mataimakin shugaban kasar ya ce matsayinsu na bai-daya shi ne cewa farashin makamashi ya yi tsada sosai.
“Za mu yi duk abin da ya dace domin rage farashin man fetur a kasar nan. Hakan ya hada da duk matakan da za mu iya dauka, har da dawo da tallafin,”
- Rabiu Kwankwaso

Source: Facebook
Mace tana takarar shugaban kasa a NRM
Rahoton nan cewa yake yi Dr. Esther Okereke ta ce maza sun gaza a Najeriya don haka lokaci ya yi da za a ba mace damar yin mulki.
‘Yar takarar shugaban kasar kuma tsohuwar 'yar wasan fim ta ce wutar lantarki da tsaro su ne gaba na idan ta shiga fadar Aso Rock.
Tsohuwar jarumar ta ce ba wai ta na neman kujera don jinsinta ba ne, talakawa ta sa a gaba don haka ta ke neman jama'a su zabe ta.
Asali: Legit.ng


