2027: Mace Ta Fito Neman Takarar Shugaban Kasa a Najeriya Ta Ce Maza Sun Gaza

2027: Mace Ta Fito Neman Takarar Shugaban Kasa a Najeriya Ta Ce Maza Sun Gaza

  • 'Yar takarar shugaban kasa ta jam'iyyar NRM, Esther Okereke, ta ce shugabannin maza da aka yi a tarihi duk sun gaza
  • Ta yi kira ga 'yan Najeriya da su ba mace damar shugabanci a zaben 2027 duba da cewa maza sun kasa kawo sauyi har yau
  • Okereke ba tallar jinsinta take yi ba, za ta fi mayar da hankali kan wutar lantarki, tsaro da rikon amana idan ta samu mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - ’Yar takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar National Rescue Movement (NRM), Esther Okereke, ta soki mulkin maza.

Dr Esther Okereke ta bukaci ’yan Najeriya su ba mace damar jagorantar kasar, abin da ba a taba yi ba tunda aka kafa kasar a tarihi.

Esther Okereke
Esther Okereke mai takarar shugaban kasa a NRM Hoto: Aporokoman
Source: Facebook

Esther Okereke tana takarar shugaban kasa

Ta ce shugabancin da maza suka yi tsawon shekaru bai samar da sakamakon da ake bukata ba kamar yadda ta fada wa tashar Channels.

Kara karanta wannan

2027: Dattijon Arewa da ya yi siyasa da Sardauna ya yi maganganu kan Tinubu

Okereke ta bayyana hakan ne ranar Laraba a shirin Sunrise Daily yayin da take magana kan shirinta na zama shugaban kasa a 2027.

‘Yar takarar ta ce ta hadu da mutanen da ke shakkar ko mace za ta iya jagorantar Najeriya.

Ta ce ta tambaye su dalilin da ya sa za su ci gaba da zaben maza idan shugabancinsu bai kawo sauyi ba na tsawon shekara da shekaru.

“Shin kuna ganin ya kamata namijin da ya gaza tsawon sama da shekaru 20 ya ci gaba? Idan ba haka ba ne, to ku ba wannan matar dama,”

- Esther Okereke

Mata suna harin zama shugaban kasa a 2027

A zaben 2027, maza ne suka fi yawa cikin ’yan takara 18 da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) ta amince da su.

Mata biyu ne kadai ke takarar shugabancin kasar. Su ne Esther Okereke ta NRM da Ada Okwori ta National Democratic Party (NDP).

Kara karanta wannan

Maganar Zainab Sheikh Jafar kan cewa mahaifinta ya yi wa Atiku bakar addu'a

Sai dai Okereke ta jaddada cewa ba jinsi ta zo tallatawa ba. Ta ce tana da tsare-tsare da shirin da za ta bi wajen ceto kasar Najeriya.

Matsalar wutar lantarki za ta fara magancewa

Okereke ta bayyana wutar lantarki a matsayin daya daga cikin muhimman matsalolin da za ta fara magancewa idan aka zabe ta a badi.

Jaridar Premium Times ta rahoto ta tana cewa ingantacciyar wutar lantarki za ta taimaka wa Najeriya ta amfana da fasahar zamani a duniya.

Take cewa rashin ingantaccen wutar lantarki a Najeriya yana kawo cikas ga kasuwanci, amfani da fasaha da bunkasar tattalin arzikin kasa.

A cewarta, kananan ’yan kasuwa kan rasa abokan hulda saboda katsewar wuta. Haka kuma, kashe kudi a sayen fetur yana tatse ribar su.

Sauran abubuwan da 'yar takarar ta sa gaba

’Yar takarar ta kuma bayyana rashin tsaro a matsayin wata matsala da za ta ba fifiko a ofis.

Ta ce wasu ’yan Najeriya da ke kasashen waje suna son dawowa gida domin zuba jari. Amma rashin tsaro yana hana su dawowa.

Okereke ta kuma soki yadda ake gyaran hanyoyi gab da zuwan shugabannin siyasa ziyara.

Kara karanta wannan

PDP ta shaida matakin da ake dauka game da cire sunayen Pantami da wasu ‘yan takara

Ta ce bai kamata a rika gyara ababen more rayuwa domin burge baki kawai ba. A maimakon haka, ya kamata a rika kula da su a kai a kai.

Idan mulki ya zo hannunta, ta sha alwashin kawo gyara a harkar kiwon lafiya da rikon amana.

Esther Okereke
Esther Okereke lokacin da NRM ta ba ta takara da hoton ta a gefe Hoto: Seprebofa M Oyeghe/Samuel Moses
Source: Facebook

Gwamna ya shiga matsala saboda shiga takarar Tinubu

Labari ya zo cewa Gwamna Ademola Adeleke ya rabu da ‘yan takaransu na jam'iyyar Accord, ya tafi tallata Bola Tinubu a APC a Osun.

Shugabannin jam’iyyar Accord sun tuna masa suna da ‘dan takaran shugaban kasa da na majalisa don haka ya fito ya yi masu bayani.

An bukaci Adeleke da shugabannin jam’iyyar na kasa su bayyana matsayinsu kafin a shiga zabe domin za su iya yi wa gidansu illa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng