Lita na Jiyo Kamshin N1500, Minista Ya Ce 'Yan Najeriya na Sayen Fetur da Arha
- Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ya ce matsakaicin farashin fetur a Najeriya ya kasance ƙasa da na Amurka da wasu ƙasashen Afirka
- Ya bayyana hakan ne yayin da ake samun raguwar farashin fetur a wasu wurare bayan faduwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya
- Lokpobiri ya ce kasancewar Najeriya ƙasar da ke hako mai da kuma samun matatar Dangote ba yana nufin farashin fetur zai kasance mai sauki kai tsaye ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ya yi magana kan farashin fetur a Najeriya.
Ministan ya ce matsakaicin farashin fetur a Najeriya har yanzu ya fi na Amurka da wasu ƙasashen Afirka sauƙi, duk da cire tallafin man fetur.

Source: Twitter
Lokpobiri ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Politics Today na Channels Tv ranar Talata, 22 ga watan Satumban 2026, inda yake kare matakin gwamnatin tarayya na tsame hannu a kasuwar ɓangaren sayar da man fetur.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya fito ya fadi gaskiya, ya ce farashin man fetur zai iya ƙara tsada a Najeriya
Farashin fetur ya kai N1,450 a wasu wurare
Kalaman ministan sun zo ne yayin da Matatar Dangote da wasu ’yan kasuwar man fetur suka fara rage farashin man da suke sayarwa daga rumbun ajiya, bayan raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Sai dai duk da wannan raguwar, ana ci gaba da sayar da litar fetur tsakanin N1,370 zuwa N1,450 a wasu wurare.
Lokpobiri ya ce farashin fetur a Najeriya ya fi na Amurka, Kamaru, Ghana da Afirka ta Kudu sauƙi.
Ya kwatanta farashin Najeriya da wasu ƙasashe
“Dauki Amurka, matsakaicin farashin litar fetur ya kai N1,633. A Najeriya, matsakaicin farashin shi ne N1,430."
“Idan ka je Kamaru, N1,959 ne. Ghana kuma N2,070, haka ma Afirka ta Kudu N2,070. Don haka matsakaicin farashin fetur a Najeriya har yanzu ya fi na waɗannan ƙasashe sauƙi,” in ji shi.
Me ya ce kan matatar Dangote?
Ministan ya ce kasancewar Najeriya ƙasar da ke hako mai, tare da samar da babbar matatar Dangote, ba yana nufin farashin fetur zai ragu kai tsaye ba.

Kara karanta wannan
An ga tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe mataimakin kwamandan rundunar tsaro a Plateau
Ya ce bayanan da ake da su sun nuna cewa Amurka ce ƙasar da ke kan gaba wajen hako mai da iskar gas a duniya, sannan tana da babbar damar tace man fetur.

Source: Facebook
Sai dai duk da hakan, ya ce farashin litar fetur a Amurka ya fi na Najeriya tsada.
“Don haka, duk da kasancewar Matatar Dangote a nan, hakan ba yana nufin farashin fetur zai kasance da arha ba saboda matatar Dangote tana nan,” in ji Lokpobiri.
Ya ƙara da cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda tsarin buɗe kasuwar ya haifar da sabuwar damar tattalin arziki a ɓangaren man fetur.
Kwankwaso ya ce za su bullo da tallafin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi maganar dawo da tallafin man fetur.
Kwankwaso ya ce gwamnatin jam’iyyar ƙarƙashin Peter Obi za ta dawo da tallafin man fetur, amma ta wata hanya daban.
Asali: Legit.ng