Zance Ya Kare, Peter Obi Ya Bayyana Matsayarsa kan Batun Dawo da Tallafin Man Fetur a Najeriya

Zance Ya Kare, Peter Obi Ya Bayyana Matsayarsa kan Batun Dawo da Tallafin Man Fetur a Najeriya

  • Dan takarar shugaban kass na jam'iyyar NDC, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo fa tallafin man fetur a Najeriya
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce an samu kusan Naira tiriliyan 16 daga cire tallafin, amma ana zargin ana almundahana da kuɗin
  • Obi ya ce shirin siyasarsa zai cire tallafin cikin tsari tare da mayar da kuɗin wajen da talakawa za su amfana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa ta NDC, ya sake jaddada goyon bayansa ga cire tallafin man fetur a Najeriya.

Matsayar Peter Obi na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan alkawarin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi na dawo da tallafin mai idan ya ci zaben 2027.

Kara karanta wannan

Bayan abubuwa sun ɗauki zafi, an fito da gaskiyar shirin Atiku na dawo da tallafin mai a Najeriya

Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Wace matsaya Peter Obi ya dauka?

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Obi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani taro da ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta shirya a Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers.

“Na amince kuma ina nan kan matsayina cewa dole ne a cire tallafin mai. Rashin iya tafiyar da kuɗin da aka samu daga hakan bai kamata ya zama dalilin da zai hana cire tallafin ba,” in ji tsohon gwamnan Anambra.

Ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta samar wa ’yan ƙasa wasu hanyoyin amfani da kuɗin da aka tara bayan cire tallafin, domin inganta walwala da jik dadinsi.

Abin da ya kamata a yi a kudin tallafin

“Abin da ya kamata mu yi shi ne, da zarar mun cire tallafin, mu samar wa mutane wasu hanyoyin amfani da kuɗin tallafin ta yadda kowa zai gani a kasa,"
“Abin da muke da shi a yau shi ne, cire tallafin da kuma kuɗaɗen da ake samu sakamakon hakan ana tafiyar da su ba daidai.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake haduwa da fushin gwamnatin Tinubu kan maido tallafin mai

"Ana ma zargin wadu ke sama da fadi da kudin. Misali, a cewarsu, mun samu Naira tiriliyan 16 daga lokacin da aka cire tallafin zuwa yanzu."

- Peter Obi.

Obi ya ce a cikin tsarin jagorancin Najeriya da ya tsara, ya yi shirin cire tallafin ne cikin tsari”, ta yadda duk kuɗin da aka samu daga cire shi za a zuba su yadda ya kamata domin amfanin talakawan ƙasa.

Obi Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi da Atiku Sbubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Tsohon gwamnan ya ce zai kawo tsari mai kyau da zai karkatar da kudaden tallafin man da aka cire zuwa bangaren da yan Najeriya musamman talakawa za su amfana, cewar rahoton Vanguard.

Peter Obi ya kaddamar da kamfe

A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi ya kalubalanci dukkan ’yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da su fito gaban ’yan Najeriya su kare tarihin ayyukansu.

Obi ya yi wannan kiran ne ranar Juma’a da ta wuce yayin wani taron manema labarai da aka gudanar domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a hukumance.

Ya ce duk wanda ke son jagorantar ƙasar dole ne ya kasance a shirye ya fuskanci ’yan Najeriya tare da barin jama’a su tantance manufofinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262