Gwamnatin Tinubu Ta Kare Farashin Mai, Ta Magantu kan Yiwuwar Dawo da Tallafi

Gwamnatin Tinubu Ta Kare Farashin Mai, Ta Magantu kan Yiwuwar Dawo da Tallafi

  • Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce rangwamen man fetur na NNPC na kwanaki 30 ba komawa tallafin mai ba ne
  • Ya bayyana cewa NNPC ta amince da rage wasu ribar da take samu domin rage wa ’yan Najeriya raɗaɗin tsadar man fetur
  • Ministan ya ce gwamnatin Tinubu na ci gaba da gyare-gyaren tattalin arziki, tare da ƙara samar da makamashi mai araha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris, ya kare shirin kamfanin NNPC na rage farashin man fetur na kwanaki 30.

Ya ce manufar shirin ita ce samar da sauƙi na ɗan lokaci ga ’yan Najeriya, sakamakon hauhawar farashin makamashi a duniya.

Gwamnatin tarayya ta magantu kan rangwame kan farashin mai
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manyan editoci da ’yan jarida wanda shafin ma'aikatar yada labarai ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ware gwamna 1 a Arewa, ta yaba masa kan ayyukan alheri

Gwamnati ta magantu kan tallafin mai

Idris ya bayyana cewa matakin ba yana nufin gwamnati ta dawo da tallafin man fetur ba ne, domin NNPC ce ta amince da rage wasu ribar da take samu.

Ya ce kamfanin ya duba ribar da yake samu, sannan ya yanke shawarar sadaukar da wani ɓangarenta domin rage wa ’yan Najeriya raɗaɗin tsadar man fetur.

Sai dai rangwamen ya jawo suka daga ’yan siyasar adawa, shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki.

Sun nuna damuwa kan tsawon lokacin da rangwamen zai ɗauka, yawan mutanen da za su amfana da shi da kuma tasirinsa ga iyalan da ke fama da tsadar rayuwa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki shirin, inda ya bayyana shi a matsayin matakin siyasa da zai samar da sauƙi na ɗan lokaci gabanin zaɓen 2027.

Atiku ya kuma tambayi dalilin da ya sa aka ɗora wa NNPC alhakin ɗaukar kuɗin rangwamen, tare da tambayar ko kwamitin gudanarwar kamfanin ya amince da matakin.

Kara karanta wannan

Ya mutane za su samu fetur mai araha a garuruwan da babu gidan man NNPC? An aika sako ga Tinubu

Ya kuma nemi a bayyana yadda za a nuna tasirin kuɗaɗen rangwamen a cikin asusun kamfanin.

Minista ya wayar da kan yan kasa kan dawo da tallafin mai
Ministan yada labarai a Najeriya, Mohammed Idris. Hoto: Federal Ministry of Information and Orientation.
Source: Twitter

Gwamnati ta yi magana kan tsadar makamashi

A jawabinsa, ministan ya amince cewa hauhawar farashin makamashi na jefa iyalai da ’yan kasuwa cikin matsin tattalin arziki.

Ya ce gwamnatin tarayya ta himmatu wajen faɗaɗa hanyoyin samun makamashi mai araha da kuma ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida.

Idris ya bayyana cewa tsadar makamashi matsala ce da ta shafi ƙasashe da dama a duniya, inda gwamnatoci ke ɗaukar matakai daban-daban domin kare tattalin arzikinsu da rage wa al’umma wahala.

Ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki, tare da ba da muhimmanci ga jin daɗin ’yan Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta yaba gwamnan Neja

Kun ji cewa Ministan Yaɗa Labarai a Najeriya Mohammed Idris, ya yi ruwan yabo ga Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago kan ayyukan alheri.

Gwamnatin tarayya na shirin kashe kusan Naira tiriliyan 1.5 wajen faɗaɗa da sake gina babbar hanyar Lambata zuwa Kontagora.

An shirya aza harsashin aikin hanyar a Bida ranar 13 ga Oktoba, domin sauƙaƙa jigilar amfanin gona da bunƙasa harkokin kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.