"Ta Wata Hanya Daban": Kwankwaso Ya Ce Za Su Dawo da Tallafin Fetur

"Ta Wata Hanya Daban": Kwankwaso Ya Ce Za Su Dawo da Tallafin Fetur

  • Rabiu Kwankwaso ya ce gwamnatin NDC ƙarƙashin Peter Obi za ta dawo da tallafin man fetur, amma ta wata hanya daban da tsarin da aka sani a baya
  • Ya ce gwamnati za ta iya zuba jari wajen gina matatun mai domin ƙara samar da fetur a cikin gida da rage farashin man fetur
  • Kwankwaso ya soki yadda gwamnatin Bola Tinubu ta cire tallafin man fetur nan take bayan kama mulki a shekarar 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi maganar dawo da tallafin man fetur.

Kwankwaso ya ce gwamnatin jam’iyyar ƙarƙashin Peter Obi za ta dawo da tallafin man fetur, amma ta wata hanya daban.

Kwankwaso ya ce za su dawo da tallafi
Peter Obi tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Kwankwaso, wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise TV ranar Talata, 22 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Obi sun samu babbar dama a kwamitin yakin neman zaben NDC

Ya na magana ne kan manufar cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar da kuma matsayoyin ’yan takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.

“Za mu dawo da tallafi ta hanya daban”

Da aka tambaye shi ko zai kasance da wahala NDC ta yi kamfen a yankin Arewa maso Yamma, inda ake samun goyon bayan dawo da tallafin man fetur, Kwankwaso ya ce jam’iyyar za ta dawo da tallafin ta hanyar da ta dace da manufofinta.

“A’a, a’a, a’a. Ku duba, za mu dawo da tallafi ta hanya daban,” in ji shi.

Da aka tambaye shi yadda za a aiwatar da hakan, Kwankwaso ya ce gwamnati za ta iya zuba jari wajen matatun mai domin ƙara samar da fetur a cikin gida, ta yadda za a samu man fetur ga ’yan Najeriya a farashi mai sauƙi.

Kwankwaso ya yi magana kan gina matatun mai

Kwankwaso ya ce akwai hanyoyi da dama da za a iya bi domin rage farashin man fetur.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnatin Najeriya sun ji wuta, sun tura wasiƙa mai zafi ga Shugaba Tinubu

Ya ce kasancewar ’yan kasuwa sun iya gina matatun mai ya nuna cewa gwamnati ma za ta iya gina nata matatun idan yanayi ya buƙata.

“Yanzu muna da matatar mai da wani ɗan kasuwa ya gina, kuma na tabbata za a ƙara gina wasu matatun,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa idan mutane masu zaman kansu za su iya gina matatun mai a ƙasar, babu dalilin da zai hana gwamnati gina nata domin cimma buƙatun ƙasar.

A cewarsa, abin da ake buƙata shi ne ’yan Najeriya a faɗin ƙasar su samu damar zuwa gidajen mai su sayi fetur a farashi mai sauƙi.

“Mu a NDC za mu yi duk abin da ya kamata domin rage farashin man fetur,” in ji Kwankwaso.

Ya soki yadda Tinubu ya cire tallafin man fetur

Kwankwaso ya ce manyan ’yan takarar shugaban ƙasa uku a zaɓen 2023, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, sun yi kamfen kan cire tallafin man fetur.

Sai dai ya soki yadda Shugaba Tinubu ya aiwatar da manufar nan take bayan hawansa mulki. A cewarsa, daga cikin manyan ’yan takarar uku, Tinubu ne ya yanke shawarar cire tallafin, kuma abin da ya yi gargadin zai biyo bayan hakan ya faru.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a NDC kan kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso da Obi

Ya ce matsalar ta ƙara tsananta ne saboda an cire tallafin tun daga ranar farko ta gwamnatin Tinubu, ba tare da an yi la’akari da wasu matsalolin da za su iya tasowa ba.

Kwankwaso ya ce wannan mataki na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mawuyacin hali.

Kwankwaso ya ce za su dawo da tallafi
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

NDC ta ba Obi da Kwankwaso dama

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NDC ta bayyana cewa tana shirye-shiryen kammala kafa kwamitin yakin neman zabenta.

Jam’iyyar ta kuma ce Obi da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, an ba su damar gabatar da sunayen mafi yawan manyan jami’an kwamitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng