"Sun Tsorata," Kwankwaso Ya Gano Masu Shirin Magudi a Zaben Shugaban Kasa na 2027
- Tsohon gwamnan Kano ya yi zargin cewa wasu na kusa da APC suna cewa za su iya rubuta sakamakon zaɓe ko da sun samu ƙuri’u 1,000 kacal
- Kwankwaso ya ce bai da hujja kai tsaye kan zargin, amma ya ji hakan daga mutanen da ke kusa da wasu jiga-jigan jam’iyyar
- Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya ce tikitin Obi da Kwankwaso ya haɗa magoya baya daga Kudu da Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi zargin cewa wasu mutane da ke kusa da jam’iyyar APC suna taƙama da cewa za su iya yin magudin sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Madugun Kwankwasiyya ya yi ikirarin cewa wadannan mutane suna takama za su iya sauya sakamakakon zabe ko da kuwa sun samu ƙuri’u 1,000 kacal.

Source: Facebook
Kwankwaso, wanda shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today ranar Alhamis.
Ya ce jam’iyya mai mulki na cikin damuwa ne saboda yadda tikitin ’yan adawa ke ƙara samun farin jini.
Sai dai ya ce ba shi da wata hujja kai tsaye da ke tabbatar da wannan zargi, yana mai bayyana cewa labarin ya same shi ne ta hannun mutanen da ke kusa da wasu jiga-jigan APC.
“Mun ji da yawa daga cikinsu, musamman ta bakin mutanen da ke kusa da su, suna taƙama kamar yadda suka saba cewa ko da sun samu ƙuri’u 1,000 ne kawai, za su rubuta sakamakon yadda suke so,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko yana da hujjar da za ta tabbatar da zargin, Kwankwaso ya amsa da cewa: “A gaskiya, muna jin hakan ne daga mutanen da ke kusa da su.”
Rabiu Kwankwaso ya fadi damuwar yan APC
Kwankwaso ya ce APC da magoya bayanta sun shiga damuwa da dimuwa ne saboda yadda ’yan adawa ke ƙara samun farin jini, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya bayyana cewa tikitin ’yan adawan ya samu karɓuwa ta dalilin farin jinin Obi a Kudancin Najeriya da kuma tasirin tafiyar Kwankwasiyya a Arewa.
Ya ce haɗuwar waɗannan sansanonin siyasa biyu ta samar da ƙungiyar da za ta iya fuskantar zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027.
Talakawa na fuskantar matsin rayuwa
Kwankwaso ya ce manyan ’yan siyasar da ke goyon bayan jam’iyya mai mulki sun nisanta kansu da halin ƙuncin rayuwa da talakawan Najeriya ke fuskanta a ƙauyuka, garuruwa da birane.

Source: Twitter
Ya ce ’yan Najeriya na cikin fushi kuma suna neman wani zaɓi na daban, yana mai bayyana kwarin gwiwarsa cewa tikitin Obi da Kwankwaso zai iya samar da sauyin da suke buƙata.
Dalilin neman Atiku ya janyewa Obi
A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa yake son Atiku Abubakar ya janyewa Peter Obi.
Kwankwaso ya ce bai yi wannan kira ne saboda yana ƙiyayya da Atiku ba, yana mai bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasar a matsayin wanda suka daɗe suna aiki tare.
Asali: Legit.ng


