Atiku Ya Gargadi Tinubu, Ya Fadi Wasu 'Yan ADC da aka Tsare a Abuja
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya gargaɗi gwamnatin tarayya kan kama ko tsare mambobin jam’iyyar ADC saboda alaƙarsu da jam’iyyar
- Atiku ya ce rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun tsare mambobin ADC uku a sashen binciken manyan laifuffuka (CID)
- Ya kuma nuna damuwa kan zargin kama ɗan Isma’il Sahabi bayan jami’an tsaro sun kasa samun mahaifinsa, inda ya buƙaci a sake shi nan take idan hakan ne ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da duk wani yunƙuri na tsoratarwa ko cin zarafin mambobin jam’iyyar ADC.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa manufofinsa da sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa ya ce rahotanni sun nuna cewa an tsare mambobin ADC uku a sashen binciken manyan laifuka na ’yan sanda (CID), yayin da kuma aka kama ɗan wani mutum mai suna Isma’il Sahabi bayan jami’an tsaro sun kasa samun mahaifinsa.
Atiku ya nemi a saki ɗan ADC
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nuna matuƙar damuwa kan rahoton kama ɗan Sahabi, yana mai cewa bai kamata a kama mutum saboda ana neman mahaifinsa ba.
The Cable ta rahoto ya ce idan jami’an tsaro sun kama yaron ne saboda sun kasa samun mahaifinsa, to ya kamata a sake shi nan take.
Atiku ya bayyana cewa bai kamata gwamnati mai mutunta doka ta tsare mutum domin amfani da shi wajen matsa wa wani na daban lamba ba.
Kiran Atiku ga 'yan sanda
Atiku ya buƙaci rundunar ’yan sandan Najeriya ta bayyana inda take tsare da mambobin ADC ukun da kuma ɗan Sahabi.
Dan takarar shugaban kasar ya kuma nemi a bayyana zargin da ake yi wa kowannensu tare da ba su damar ganin iyalansu da lauyoyinsu.

Source: Facebook
A cewarsa, duk wanda babu sahihin zargin aikata laifi a kansa ya kamata a sake shi, yayin da idan akwai hujjar aikata laifi, sai a gabatar da ita a gaban kotu.
A korafin da ya yi, Atiku Abubakar ya bayyana cewa katin zama ɗan jam’iyyar ADC ba laifin da za a kama mutum a kansa ba ne.
An yi shari'ar ADC a Gombe
A wani labarin, kun ji cewa ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dukku/Nafada a jihar Gombe, Hon. Abdullahi El-Raheed, ya samu nasara a shari’ar da aka shigar domin ƙalubalantar cancantarsa ta tsayawa takara a zaɓen 2027.
Mai shari’a a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yi watsi da ƙarar ne saboda rashin hujjoji, kamar yadda ɗan majalisar ya bayyana.
Bayan hukuncin, El-Raheed ya gode wa Allah da magoya bayansa, sannan ya miƙa hannun sulhu ga ɗan siyasar da ya kai shi ƙara, yana mai neman su haɗa kai domin ci gaban mazabar Dukku/Nafada.
Asali: Legit.ng