Atiku Ya Kawo Sabon Tsarin Kamfen, zai Rika Magana da Talakawa Kai Tsaye
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da shafin Ask AA domin bai wa 'yan Najeriya damar yi masa tambayoyi kai tsaye
- Shafin zai bai wa jama'a damar tambayar Atiku kan tattalin arziki, tsaro, fasaha, samar da ayyukan yi da shirye-shiryensa na rage tsadar rayuwa
- Daraktan yaɗa labaran yaƙin neman zaɓen Atiku ya ce za a kuma samar da hanyar amfani da rediyo domin kai shafin ga al'ummomin da ba su da damar amfani da intanet
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da wani shafin intanet mai suna Ask AA, domin bai wa 'yan Najeriya damar yi masa tambayoyi kan manufofinsa da shirye-shiryensa na shugabancin ƙasa.
Atiku, wanda yake takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar ADC, ya ce shafin zai ba jama'a damar samun bayanai kan matsayinsa game da muhimman batutuwan ƙasa.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Atiku ya ce an tsara buɗe shafin ne da ƙarfe 8:30 na dare a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026.
Za a iya amfani da shi kyauta, inda Atiku da kansa zai amsa wasu tambayoyi, tare da taimakon tawagar yaɗa labaransa.
Za a rika yi wa Atiku tambayoyi
Shafin Ask AA zai bai wa 'yan Najeriya damar tambayar Atiku kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, tsaro, fasaha, samar da ayyukan yi da kuma shirye-shiryen rage tsadar rayuwa.
Haka kuma, za a iya amfani da shafin wajen neman ƙarin bayani kan tarihin Atiku a harkokin mulki, manufofinsa da kuma shawarwarin da jama'a ke da su kan ci gaban Najeriya.
Atiku ya bayyana cewa zai kira wasu daga cikin mutanen da suka bar bayanan tuntuɓarsu domin jin ƙorafinsu da fahimtar matsalolin da suke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum.
A cewarsa, shirin zai taimaka wajen samar da tattaunawa kai tsaye tsakanin shugabanni da jama'a, ba tare da wasu mutane sun shiga tsakani ba.
Dalilin ƙaddamar da shafin Ask AA
Daraktan yaɗa labaran dabarun yaƙin neman zaɓen Atiku na jam'iyyar ADC, Phrank Shaibu, ya ce an ƙirƙiri shafin ne domin rage gibin bayanai tsakanin ɗan takarar da masu zaɓe.
Shaibu ya bayyana cewa manufar shirin ita ce kusantar da Atiku ga masu zaɓe ta hanyar samar da wata hanya da za su iya amfani da ita wajen tambayoyi da tattaunawa kan matsalolin ƙasa.
Ya ƙara da cewa shirin ya nuna aniyar Atiku na amfani da fasahar zamani wajen inganta ayyukan gwamnati, tsaro da kuma gudanar da mulki yadda ya kamata.

Source: Facebook
Za a samar da hanyar amfani da rediyo
Sanarwar ta bayyana cewa za a kuma samar da hanyar amfani da rediyo domin al'ummomin da ba su da damar shiga intanet su samu damar amfana da shirin.
Atiku ya ce ya ƙirƙiri Ask AA ne saboda imaninsa cewa ya kamata shugabanci ya kasance tattaunawa tsakanin ɓangarori biyu, wato shugabanni da waɗanda suke jagoranta.
A cikin saƙon da ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya bayyana cewa gudanar da mulki ya daɗe yana zama kamar wani abu mai nisa ga jama'a, saboda katangar da tsarin hukumomi ya gina tsakanin shugabanni da al'umma.
Ga bayanin da Atiku ya yi a kasa:
Hadimin Atiku ya soki Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Kenneth Okonkwo ya yi magana kan matakin Shugaba Bola Tinubu na rashin halartar yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC gaba daya.
Okonkwo, wanda ɗan wasan kwaikwayo ne da ya shiga siyasa ya yi iƙirarin cewa rashin halartar taron na nuna gazawar Tinubu ta fuskar ƙarfin jiki na gudanar da yaƙin neman zaɓe.
Ya ce ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya bayyana abin da ya kira rashin ƙarfin jikin shugaban ƙasar na gudanar da gagarumin yaƙin neman zaɓe a faɗin Najeriya.
Asali: Legit.ng


