Zaben 2027: Kwankwaso Ya Yi Hasashen Nasarar Bola Tinubu a Najeria
- Musa Illiyasu Kwankwaso ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bisa haɗin kan jam’iyyu.
- Jigon APC ya ce fitowar ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa daban-daban na nuna goyon baya ga Tinubu da sauye-sauyen tattalin arzikinsa.
- Kwankwaso ya bayyana fatan cewa ’yan siyasa a Kano za su haɗa kai wajen marawa Tinubu baya, tare da goyon bayan wa’adin Abba Yusuf na biyu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani jigo a jam’iyyar APC kuma mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, Dakta Musa Illiyasu Kwankwaso, ya yi hasashen zaben 2027.
Ilyasu Kwankwaso ya ce Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bisa haɗin kan jam’iyyu daban-daban da ke ƙara goyon bayansa.

Source: Facebook
Kwankwaso, wanda shi ne Daraktan Kuɗi na Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jama’are, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Abuja, cewar The Nation.
Ilyasu Kwankwaso ya magantu kan adawa
Jigon APC ɗin ya lura cewa shigowar manyan ’yan siyasar adawa daga sassa daban-daban na siyasa na nuna goyon baya na musamman ga shugabancin Tinubu da ajandar sauye-sauyen tattalin arzikinsa.
A cewarsa, manyan ’yan siyasa daga jam’iyyun APGA, Labour Party (LP), PDP da Accord Party sun shiga cikin wannan haɗin kai, lamarin da ya ƙarfafa tsarin yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Tinubu tun kafin lokacin zaɓe.
Da yake nuna kwarin gwiwa kan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da aka ƙaddamar kwanan nan, Kwankwaso ya bayyana irin goyon bayan da yake samu daga jam’iyyu daban-daban a matsayin abin tarihi.
Kwankwaso ya ce:
“A ganina, ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa tamkar taron jama’a ne da suka hallara domin murnar sake zaɓen Shugaba Tinubu zuwa kan mulki.
"Me kuma ya rage idan ’yan Najeriya da ya kamata mu nemi ƙuri’unsu sun fito gaba ɗaya suna goyon bayan mutum ɗaya, wato Tinubu?”

Source: Facebook
Tarihin da Tinubu ya kafa a siyasar Najeriya
Kwankwaso ya jaddada cewa babu wani shugaban ƙasa mai ci a tarihin siyasar Najeriya da ya taɓa haɗa irin wannan gagarumin haɗin gwiwa da ya ƙunshi tsoffin abokan hamayyar siyasa.
Ya ƙara da cewa:
“Ba a taɓa samun hakan a tarihin siyasar Najeriya ba, inda mutum ɗaya ya jawo kusan dukkan jam’iyyun adawa, ba ’yan siyasar adawa kawai ba, har da mutanen da ba su taɓa yarda su zauna tare ba, amma saboda Tinubu sun amince su haɗu domin cimma manufa ɗaya.”
Kwankwaso ya ambaci kalaman goyon baya daga wasu fitattun mutane, ciki har da Gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo, yana mai cewa manyan ’yan siyasa na ƙara fahimtar yanayin tattalin arzikin duniya da kuma buƙatar sauye-sauyen da Tinubu ke aiwatarwa.
Ya bayyana cewa bai kamata a ɗauki zaɓen 2027 a matsayin fafatawar neman kujerar siyasa kawai ba, sai dai a matsayin muhimmin lokaci da Najeriya za ta ƙarfafa sauyin tattalin arzikin da take ciki, cewar Punch.
Ilyasu Kwankwaso ya hasashen siyasa a Nijeriya
A wani labarin, an ji cewa Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce ayyukan da Gwamnatin Tinubu ke yi a Arewa ne ya sa manyan yan siyasa ke tururuwar komawa APC.
Tsohon kwamishinan na Kano ya jero wasu manyan ayyuka da Tinubu ya fara aiwatarwa a Kano da wasu jihohi a Arewacin Najeriya.
Musa Kwankwaso ya bayyana cewa akwai manyan yan siyasa da za su baro jam'iyyun adawa, su koma APC daga nan zuwa karshen 2025.
Asali: Legit.ng


