Tsohon Dan Majalisa Ya Bukaci Atiku da Peter Obi Sun Janyewa Tinubu, Ya Kawo Hujja

Tsohon Dan Majalisa Ya Bukaci Atiku da Peter Obi Sun Janyewa Tinubu, Ya Kawo Hujja

  • Tsohon ɗan majalisar Legas, Jude Idimogu ya nemi Atiku Abubakar da Peter Obi su janye daga takara su marawa Tinubu baya
  • Hon. Idimogu ya ce shekaru huɗu ba su isa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala sauye-sauyen da yake yi ba
  • Ya yi kira ga Arewa ta jira har zuwa 2031 kafin ta nemi shugabancin Najeriya, yana cewa ya yi imanin APC za ta lashe zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon ɗan majalisar dokokin Jihar Legas, Hon. Jude Idimogu, ya roƙi ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, da na NDC, Peter Obi, su janye daga takara su marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.

Hon. Idimogu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a yayin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An buɗe wa Tinubu ƙofar da zai iya raba Atiku da mataimakinsa kafin zaɓen 2027

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin faretin sojoji a Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, Idimogu ya ce shekaru huɗu ba za su isa Tinubu ya kammala sauye-sauyen da yake aiwatarwa ba.

Ya kara da cewa shugaban na buƙatar goyon baya da addu’o’in ’yan Najeriya domin ya cimma manufofin Ajandar Renewed Hope.

Idimogu ya nemi Atiku, Obi su janye

Idimogu ya roƙi Atiku da ya hakura da takararsa, yana mai jaddada daɗewar abota tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasar da Tinubu.

“Tinubu da Atiku sun kasance abokai tun dadewa, ba lokacin Arewa ba ne yanzu, su jira har zuwa 2031 su marawa Asiwaju baya a yanzu,” in ji shi.

Ya kuma roƙi Peter Obi, wanda ya bayyana a matsayin ɗan’uwansa, da ya marawa Tinubu baya domin tabbatar da haɗin kan kudancin Najeriya.

“Game da ɗan’uwana Peter Obi, mutum ne mai mutunci. Amma ya kamata ya bar Kudu ta yi aiki tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Idan kuka raba kan Kudu yanzu, kuna tura mulki ne zuwa Arewa,” in ji Idimogu.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata mutanen Tinubu, sun yi masa raddi mai zafi

Ya kare sauye-sauyen Tinubu

Da yake magana kan sauye-sauyen da Tinubu ke yi, Idimogu ya ce:

“Ba a gina kasa a rana ɗaya, har yanzu na yi imani da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na yi imani da ƙwarewarsa.
“Ya kamata ’yan Najeriya kada su manta cewa shekaru sama da uku kacal kenan da ya hau mulki, kuma ba zai iya yin abin al’ajabi ba. Tare da dukkan sauye-sauyen da yake aiwatarwa, zai ɗauki lokaci kafin amfaninsu ya kai ga talakawan Najeriya,” in ji shi.
Peter Obi.
Manyan yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun adawa, Peter Obi da Atiku Abubakar Hoto: Peter Obi, Atiku Abubakar
Source: Facebook

Idimogu ya bayyana Tinubu a matsayin ɗan Najeriya mai kishin ƙasa wanda ya himmatu wajen ciyar da ƙasar gaba, sannan ya yi kira ga ’yan ƙasa a sassa daban-daban da su mara masa baya.

An yi hasashen nasarar Tinubu a 2027

Kun ji cewa mujallar The Economist ta ce Shugaba Bola Tinubu na iya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 duk da yadda jama'a suka juya masa baya.

Mujallar ta danganta wannan yiwuwar da tsarin siyasar Najeriya, fa’idar kasancewar Tinubu kan kujerar shugaban ƙasa da kuma rarrabuwar jam’iyyun adawa.q

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262