‘Nadamar da APC Za Ta Yi a Ranar Zabe’: Kwankwaso Ya Jaddada Kwarin Guiwarsu
- Rabiu Kwankwaso ya soki gwamnoni 31 da suka mara wa Tinubu baya a zaɓen 2027, yana zargin ba su da ƙarfin cin zaɓe da kansu
- Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya ce farin jinin Peter Obi a Kudu da ƙaruwar tasirin jam’iyyar a Arewa na damun APC
- Kwankwaso ya danganta raguwar farin jinin Tinubu da APC da tsadar rayuwa da rashin tsaro, sannan ya nuna fargabar yiwuwar maguɗin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Kwankwaso, ya caccaki mulkin jam'iyyar APC.
Kwankwaso ya soki gwamnoni 31 da suka mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin ya sake tsayawa takara.

Source: Twitter
Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a daren Alhamis.

Kara karanta wannan
"Sun tsorata," Kwankwaso ya gano sasu shirin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
Yadda gwamnoni 31 suke goyon bayan Tinubu
An ruwaito ruwaito cewa aƙalla gwamnoni 31 ne suka fito fili suka amince da sake zaɓen Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a 2027.
Wasu daga cikin gwamnonin, kamar Ademola Adeleke na Osun da Charles Soludo na Anambra, ba ’yan jam’iyyar APC ba ne.
Da yake magana a shirin, Kwankwaso ya ce Tinubu da gwamnonin sun haɗa kai gabanin zaɓen 2027 ne saboda ba su da tabbacin za su iya cin zaɓe da kansu.
Ya ce:
"na ganin gwamnoni da dama suna yin manyan kura-kurai, har ma sun fara ganin cewa ba su da ƙwarewar da za su iya cin zaɓe da kansu.”
"Saboda haka, sai suka jingina kansu ga shugaban ƙasa. Ina kuma ganin shugaban ƙasar yana tunanin ba zai iya cin zaɓe shi kaɗai ba, don haka dole ya jingina ga gwamnonin, APC da gwamnoni suna fargabar NDC da farin jinin Peter Obi’"

Source: Facebook
Kwankwaso ya tuna farin jinin Peter Obi
Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, yana da farin jini sosai a Kudancin Najeriya gabanin zaɓen 2027.
Ya kuma ce jam’iyyar ta samu gindin zama a Arewacin Najeriya, tare da gina ƙungiya mai ƙarfi ta hanyar haɗa mutanen da ke son samar da mafita ga matsalolin ƙasar.
Tsohon gwamnan ya yi imanin cewa wannan ƙaruwar farin jinin NDC na damun gwamnonin da ke goyon bayan sake zaɓen Tinubu.
Kwankwaso ya ce farin jinin Tinubu da APC ya ragu saboda ƙarin wahalhalun rayuwa da tabarbarewar tsaro da ake fuskanta a faɗin Najeriya.
Kwankwaso ya gano shirin magudin zabe
An ji cewa tsohon gwamnan Kano ya yi zargin cewa wasu na kusa da APC suna cewa za su iya rubuta sakamakon zaɓe ko da sun samu ƙuri’u 1,000 kacal.
Kwankwaso ya ce bai da hujja kai tsaye kan zargin, amma ya ji hakan daga mutanen da ke kusa da wasu jiga-jigan jam’iyyar.
Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC ya ce tikitin Obi da Kwankwaso ya haɗa magoya baya daga Kudu da Arewa.
Asali: Legit.ng
