Wajen Rantsar da Kwamitin Kamfe Ya Zama Matattarar Habaici tsakanin Akpabio, Wike da gwamnoni

Wajen Rantsar da Kwamitin Kamfe Ya Zama Matattarar Habaici tsakanin Akpabio, Wike da gwamnoni

  • Maimakon hankali ya karkata wurin shirin kamfe, an ji yadda aka rika jifan juna da maganganu a Aso Rock
  • Manyan ‘yan siyasa sun yi wa junansu habaici da za a rantsar da kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu
  • Godswill Akpabio, Hope Uzodinma da Nyesom Wike sun yi amfani da taron wajen aman abin da yake ransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Rikicin siyasa ya fito fili a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja ranar Laraba da ake kaddamar da kwamitin yakin neman zaben APC.

Hakan ya faru ne da Ministan Abuja, Nyesom Wike, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da wasu suka yi maganganu a Aso Rock.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da mai dakinsa wajen kaddamar da kwamitin kamfe Hoto: Bayo Onanuga
Source: Instagram

An aika wa Gwamna Hope Uzodinma sako

Daily Trust ta rahoto yadda shugabannin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, suka yi kalamai da ake ganin suna caccakar juna.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike ya sake fallasa abin da wasu daga cikin gwamnoni suka yi masa

Kalaman sun nuna cewa akwai bambancin ra'ayi tsakanin manyan ‘yan siyasar da ke goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a APC.

Ko da yake Wike da Sanata Akpabio ba su ambaci sunan Uzodimma kai tsaye ba, lokacin da suka yi jawabi, an gane inda suka dosa.

Nyesom Wike ya kalubalanci gwamnonin APC

Wike, wanda dan jam'iyyar adawa ta PDP ne ya kalubalanci gwamnonin APC da su tabbatar cewa shugaban kasa ya samu nasara a jihohinsu.

Ya gargade su cewa kasancewa cikin majalisar yakin neman zabe ba yana nufin sun yi nasarar siyasa ba sai jiharsu ta shiga hannun APC.

Watakila wannan hannunka mai sanda ne ga gwamnonin da suke yaki da Wike saboda kawai ganin suna APC shi kuma ‘dan PDP ne.

Rikicin Gwamnonin APC da tafiyar Wike

Tafiyar Rainbow Coalition da ya kafa domin goyon bayan Tinubu tana shan suka daga kungiyar PGF.

A watan Satumba, Uzodimma, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC, ya nuna gwamnonin jam'iyyar ba su tare da tafiyar Wike.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen mutane 155 da za su taya Gwamna Abba yakin neman zaben Kano

Bayan bayyana wannan matsaya, Wike ya soki Uzodimma a bainar jama'a. Ya zarge shi da kasa samar wa Tinubu isassun kuri'u a zaɓen 2023.

Tsohon gwamnan Rivers din ya kuma yi masa gorin yadda PDP ta taimaki gwamnan da yake neman zarcewa.

Bayan haka, ministan ya bayyana cewa ba zai taba goyon bayan iUzodimma ya zama shugaban Majalisar Dattawa ba, abin da ake zargi yana hari.

Akpabio ya yi maganar shugabancin Majalisar Dattawa

A nasa jawabin, Akpabio, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar yakin zabe na I, ya yi zancen neman shugabancin majalisa a 2027.

Tsohon gwamnan ya gargadi gwamnoni da kada su yi watsi da mutanensu saboda neman wasu mukaman siyasa a 2023 da ba lallai su samu ba.

Akpabio ya yi amfani da batun gogewarsa a matsayin tsohon gwamnan Akwa Ibom wajen isar da sakon da ake zargin ya aika shi ne ga Uzodinma.

"Ya ku 'yan'uwana gwamnonin jihohi, ina so ku sani cewa bai kamata ku yi watsi da mutanenku ba. Na yi shekara takwas a matsayin gwamna, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Babu bukatar fara kwadayin wani mukamin da ba ku da tabbacin samu,"

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Abin da Tinubu ya faɗa wa taron ƴan tsintsiya kan shirin kamfen

- in ji Godswill Akpabio

Uzodimma ya tallata dukkan 'yan takaran APC

A nasa jawabin shi kuma, Hope Uzodimma, wanda shi ne sakataren majalisar, ya yi amfani da kalamai masu natsuwa wajen isar da sakonsa.

Ya yi kira ga hadin kai, amma ya sake jaddada cewa dukkan 'yan takarar APC sun cancanci goyon bayan jam'iyyar, ba Tinubu kadai ba.

Wannan matsaya ta saba da tsarin Rainbow Coalition, wanda gamayyar jam’iyyu ne masu tallar Tinubu.

Bola Tinubu
Nyesom Wike yana gaisawa da Bola Tinubu ranar rantsar da kwamitin kamfe a Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamna zai bar ofis ya tafi takarar sanata

Dama can an ji labari Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya amsa kiran al'ummarsa na neman kujerar Sanata duk da wa'adinsa da saura tukuna.

Akwai rade-radin cewa yana shirin yin murabus daga kan kujerar gwamna don cimma wannan muradi da fatan zama shugaban majalisar dattawa.

Za a rantsar da majalisa kafin wa'adin Uzodinma ya cika, amma da alama ya hakura da ragowar watannin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng