Rikici na Nema Ballewa tsakanin Shugaban Majalisar Dattawa da Wasu Gwamnonin APC
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ta taɓo wasu gwamnonin jam’iyyar APC a wurin kaddamar da kwamitin kamfe
- Akpabio ya bukaci gwamnonin da su mayar da hankali wajen kammala wa’adin mulkinsu na shekaru takwas kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada
- Ya ce nasarar da ya samu a siyasa tsawon shekaru 25 ta samo asali ne daga yadda yake tsayawa tare da al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja – Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya gargadi gwamnonin jam’iyyar APC) da kada su yi watsi da al’ummarsu saboda neman wasu mukaman siyasa da ba za su samu ba.
Akpabio ya yi wannan gargadi ne a ranar Laraba, yayin bikin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, wanda aka gudanar a zauren liyafa na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Source: Facebook
A rahoton Daily Trust, Akpabio ya bukaci gwamnonin da su mayar da hankali wajen kammala wa’adin mulkinsu na shekaru takwas, wanda kundin tsarin mulki ya ba su damar yi.
Nasihar Akpabio ga gwamnonin APC
Akpabio ya ce:
“Ga ’yan’uwana gwamnonin, ina so ku sani cewa bai kamata ku yi watsi da al’ummarku ba.
“Na yi shekaru takwas a matsayin gwamna. Kundin tsarin mulki ya ce ya kamata ku yi shekaru takwas. Babu bukatar ku fara neman wani mukami da ba za ku samu na,” in ji shi.
Kalaman na zuwa ne yayin da ake rade-radin shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan Imo, Hope Uzodinma, wanda ke neman zama sanata a 2027, na harin kujerar shugaban Majalisar dattawa.
Akpabio ya yi magana kan nasararsa
Akpabio, wanda ya mulki jihar Akwa Ibom daga 2007 zuwa 2015, ya ce nasarorin da ya samu a siyasa cikin shekaru 25 da suka gabata sun samo asali ne daga jajircewarsa wajen tsayawa tare da al’umma.
Ya ce:
“Ina da mutane da yawa daga daya daga cikin jihohin nan a nan, amma dole ne ku amince da gaskiya. Ku yarda da abin da nake fada muku, na shafe sama da shekaru 25 ina wannan harkar, kuma a kullum ina samun nasara.
“Dalilin da ya sa nake samun nasara shi ne saboda ina tsayawa tare da mutane. Ku je ku gyara tufafinku idan ba su yage ba.”
Sabuwar dokar Majalisar dattawa
A wasu watannin da suka gabata, Majalisar Dattawa ta yi wa dokokinta kwaskwarima kan neman kujerun shugabanci.
Dokar ta tanadi cewa sanatocin da suka yi aƙalla shekaru takwas a majalisar, kwatankwacin wa’adi biyu a jere, ne kawai za su cancanci tsayawa takarar shugabancin Majalisar Dattawa da mataimakin shugabanta.
Akwai rahotannin da ba a tabbatar da su ba da ke cewa wani gwamna, wanda wa’adin mulkinsa zai ci gaba har lokacin rantsar da Majalisar Dattawa ta 11, yana zawarcin kujerar shugaban majalisar.

Source: Facebook
Sai dai ba a tabbatar da ko Akpabio yana magana ne kan wannan gwamna ba, wanda yana cikin wadanda suka hau kan dandamali suka gabatar da jawabi ya yi nasa jawabin.
Rahotannin sun nuna cewa gwamnan na shirin yin murabus domin tsayawa takarar kujerar sanata, a matsayin wani mataki na cimma burinsa na maye gurbin Akpabio.
Akpabio ya ja hankalin yan Arewa
Kun ji cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bukaci ‘yan Najeriya, musamman matasan Arewa, su goyi bayan sauye-sauyen tattalin arzikin Bola Tinubu.
Akpabio ya ce manufofin gwamnatin Tinubu sun riga sun tsallake wani muhimmin mataki, inda ake fara ganin alamun sakamako mai kyau.
Asali: Legit.ng


