Muhimman abubuwa 7 game da sabon gwamnan jahar Imo, Hope Uzodinma

Muhimman abubuwa 7 game da sabon gwamnan jahar Imo, Hope Uzodinma

Da yammacin Talata, 14 ga watan Janairu ne Alkalan kotun koli suka tabbatar da haramcin nasarar da Gwamna Ihedioha ya samu a zaben 2019, don haka ta tsige shi, sa’annan ta tabbatar sanar da Sanata Hope Uzodinma a matsayin halastaccen zababben gwamnan jahar.

Majalisar Alkalan kotun koli guda bakwai a karkashin jagorancin babban Alkalin Alkalai, Mai sharia Tanko Muhammad ne suka zartar da hukuncin, inda suka ce Sanata Hope ya lashe zaben ranar 9 ga watan Maris.

KU KARANTA: Wata sabuwa: An garkame fadar gwamnatin jahar Imo bayan hukuncin kotun koli daya tsige gwamnan

Da wannan ne Legit.ng ta kawo muku wasu sabbin bayanai game da Gwamna mai jiran gado, Hope Uzodinma, da yake ba’a kai ga rantsar da shi ba zuwa lokacin hada wannan rahoto.

- A ranar 12 ga watan Disambar shekarar 1958 aka haifi Hope

- Dan asalin kauyen Omumma ne, dake karamar hukumar Orlu

- Ya taba wakiltar mazabar Orlu a majalisar dattawa a shekarar 2011 da 2015

- Ya yi karatun sakandari a Mgbidi Secondary School Mgbidi a shekarar 1982

- Yana da mata da yara 2

- Hamshakin dan kasuwa ne

- A matsayin san a Sanata ya jagoranci kwamitocin sufurin jirgin sama, jirgin ruwa da kasafin kudi

A wani labari kuma, sabon gwamna Hope Uzodinma, ya ce kotu ta dawo masa da hakkinsa. Uzodinma, wanda yayi magana ta bakin mai magana da yawunsa, Declan Emelumba, ya ce tun kafin rana irin ta yau ya kasance mai imani da Alkalan Najeriya.

Yace: "A yau, kotu mafi girma a kasar nan ta dawo mini da hakkin na da al'ummar jihar Imo suka bani. Hakan na nufin cewa nasarar da al'ummar jihar Imo suka bani, amma aka kwace min, ya daow. Ina mmai godiya ga Allah madaukaki,"

Ana sa ran a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu Hope zai karbi rantsuwar fara aiki a matsayin sabon gwamnan jahar Imo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel