Yahaya Bello Ya Fadi Matakin da Ya Kamata El Rufa'i Ya Dauka kafin Tsare Shi
- Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya ce yana da tabbacin kayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a zaben Majalisar Dattawa na 2027
- Bello ya ce da ya samu damar tattaunawa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kafin fara shari’o’insa, da ya shawarce shi ya rage magana
- Hakan na zuwa ne yayin da Nasir E-Rufa'i ke fuskantar shari'o'i ta tare da tsare shi ba tare da yanke masa hukunci ko ba shi beli ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa zai kayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a zaben Majalisar Dattawa mai zuwa na 2027.
Ya ce nasarorin da ya samu a lokacin da yake gwamnan Kogi da kuma gogewarsa a siyasa sun isa su nuna irin karfin da yake da shi a zaben.

Source: Facebook
Yahaya Bello ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a.
Yahaya Bello ya ce zai kayar da Natasha
Tsohon gwamnan ya yi ikirarin cewa mutanen yankinsa na bukatar shugabancin siyasa, kuma suna son ya koma Majalisar Dattawa domin ya wakilce su.
A hirar da aka yi da shi, ya kuma bayyana cewa farin jininsa ya karu tun bayan barin kujerar gwamnan jihar Kogi, inda ya ce zai kwarfe Sanata Natasha
Sai dai Bello bai bayar da karin bayani kan irin nasarorin da yake ganin za su taimaka masa wajen kayar da Akpoti-Uduaghan ba.
Shawarar da zai ba El-Rufai
A yayin hirar, Bello ya ce da ya samu damar tattaunawa da Nasir El-Rufai kafin fara fuskantar matsalolin shari’a, da ya shawarce shi ya rage magana.
Ya ce zai kuma bukaci tsohon gwamnan Kaduna ya ci gaba da zama a jam’iyyar APC, wadda ya taka rawa wajen kafawa, sannan ya jira ya ga matakin da Shugaba Bola Tinubu zai dauka.

Kara karanta wannan
Kano ta ɗauki zafi, Gwamna Abba ya yi kalaman da ake zargin ya nuna ya saki matarsa
Yahaya Bello ya bayyana El-Rufai a matsayin mutum mai daraja da akida, wanda ke dagewa wajen bin duk abin da ya yi imani da shi.
Ya ce duk da cewa ba ya fatan El-Rufai ya shiga matsala mai tsanani, ya kamata tsohon gwamnan ya koyi yadda ake tafiyar da bambancin ra’ayi a siyasa.

Source: Facebook
A halin yanzu, El-Rufai na fuskantar shari’o’i da suka shafi Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).
An yi gargadi kan zaben 2027
A wani labarin, mun rahoto cewa Majalisar Koli kan Shari’a a Najeriya ta gargadi ’yan siyasa kan daukar matakan da ka iya haddasa tashin hankali gabanin zaben 2027.
Majalisar ta ce babu wani burin siyasa da ya kai a rasa rayukan ’yan Najeriya, inda ta bukaci masu ruwa da tsaki su tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe.
Ta kuma bukaci ’yan Najeriya da suka cancanci kada kuri’a su mallaki katin zabe tare da kada kuri’unsu ga ’yan takarar da suka zaba.
Asali: Legit.ng
