Maganar Zainab Sheikh Jafar kan Cewa Mahaifinta Ya Yi wa Atiku Bakar Addu'a
- Ɗiyar marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam, Zainab, ta fito neman bayani da kuma bidiyon shaidar cewa mahaifinta ya yi wa wani ɗan siyasa addu'ar rashin samun mulki
- Zainab ta bayyana cewa tambayarta ba ta siyasa ba ce, illa kawai bin umarnin Allah ne na yin bincike don samun tabbaci kan labaran da ake yaɗawa da baki
- Wannan tambaya ta jawo hankalin mutane da dama a kafafen sada zumunta, inda ma'abuta amfani da kafafen suka bayyana ra'ayoyinsu mabanbanta tare da goyon bayan bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Ɗiyar shahararren malamin addinin Musulunci, marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam, Zainab Jafar, ta buƙaci a ba ta tabbaci kan wani labari da ake yaɗawa da baki dangane da mahaifinta.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da yada jita-jita game da addu'ar da ake cewa marigayin malamin ya yi wa wani dan siyasa.

Source: Facebook
Zainab ta wallafa tambayarta ne a dandalin Facebook domin neman sanin ko akwai bidiyon inda Sheikh Jafar ya yi wa wani ɗan takarar shugaban ƙasa addu'ar cewa:
"Allah Ya sanya mishi son mulki kuma ya hana shi samun mulkin".
Tambayar Zainab Jafar Mahmud Adam
Zainab ta ƙara jaddada cewa neman bayanin ba shi da alaƙa da harkar siyasa ta ko wane nau'i, tana mai cewa:
"Tambaya ce ba siyasa ba. Bisa umarnin Allah na in an zo mana da labari to mu yi bincike domin samun tabbaci. Tambayar ita ce: Don Allah akwai mai bidiyo ɗin wannan maganar ya taimaka min da shi? Ko kuwa dai labarin na baki ne kaɗai?
Ta kammala da cewa:
'Ba ma siyasa ko a fili ko a boye,"
Tambayar Zainab ta bijiro ne a daidai lokacin da ake tunkarar zaɓen 2027, inda wasu ke zargin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, malamin ya yi wa wannan addu'ar a shekarun baya.
Martanin jama'a da masu sharhi
Al'umma daban-daban sun bayyana ra'ayoyinsu game da lamarin, inda Muh'd IB Ahmad Baban-Joda ke cewa sharrin 'yan Najeriya ya wuce ƙa'ida musamman a harkar siyasa da kasuwanci.
A gefe guda, Aminu M Inuwa ya bayyana cewa:
"Maganar ma ba Atiku aka yi wa ba. Sheikh Jafar da Adamu Ciroma yake yi bayan an jefi Atiku a Kano lokacin. Ciroma ya ce ai an taɓa jifan Annabi a Ta'if, ba a kan Atiku aka fara jifan shugaba ba. To meye laifin Atiku a nan?"
Adam Sharada shi ma ya goyi bayan neman bidiyon inda ya ce:
"Nima zan yi farin ciki da samu idan akwai. Na saurari huɗubobin Shaikh Ja'afar masu tarin yawa, har da huɗubar 'Illar Harshe', amma ban kai ga jin wannan zancen ba. Muna fatan idan akwai a samu saboda tahƙiƙi!"

Source: Original
Babu dan takarar NDC a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta su kwantar da hankali sakamakon rashin sa sunan ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Aminu Gwarzo a cikin 'yan takara.
Ƙungiyar ta nuna kwarin gwiwar cewa za a warware matsalar ta hanyar tsarin gudanarwa da na shari'a da ake da su, tana mai buƙatar jam'iyyar NDC da ta ɗauki matakin gaggawa domin kare muradun 'yan takarar.
Kakakin ƙungiyar, Dr. Habibu Sale Mohammed, ya bayyana a ranar Lahadi cewa abin da ya faru ya haifar da damuwa tsakanin magoya baya, amma ya yi kashedi a kan jita-jita da yaɗa labaran da ba su inganta ba.
Asali: Legit.ng


