‘Ku Cire Rai kan Dawo da Tallafin Mai’: Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Zare Idanu

‘Ku Cire Rai kan Dawo da Tallafin Mai’: Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Zare Idanu

  • Daya daga cikin masu neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NRM, ta yi magana kan dawo da tallafin man fetur
  • Ta bayyana cewa babban ƙalubalen cire tallafin shi ne tabbatar da gaskiya da kuma yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka samu
  • Okereke ta yi kira ga gwamnati da ta karkatar da kuɗaɗen tallafin zuwa ayyukan raya ƙasa, inganta walwala da samar da ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - ’Yar takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar National Rescue Movement (NRM), Dakta Esther Okereke, ta yi magana kan dawo da tallafin mai.

Yar takarar shugaban kasar ta ce gwamnatinta ba za ta dawo da tallafin man fetur ba idan aka zaɓe ta.

Okereke ta magantu kan dawoda tallafi a gwamnatinta
Daya daga cikin yan takarar shugaban kasa a Najeriya, Esther Okereke. Hoto: Esther Okereke.
Source: Facebook

Okereke ta bayyana hakan ne yayin da ta fito a shirin tattaunawa da manyan mutane na Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a ranar Lahadi a Abuja.

Kara karanta wannan

Kano: NDC ta yi mamakin cire sunan Gwarzo, ta faɗi tabbacin da INEC ta ba ta

Dalilin Okereke na kin dawo da tallafi

Ta ce a maimakon dawo da tallafin, gwamnatinta za ta tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin sun amfanar da dukkan ’yan Najeriya, ba wasu tsiraru masu gata kawai ba.

’Yar takarar ta ce duk da cewa cire tallafin man fetur ya riga ya shafi rayuwar ’yan Najeriya, babban ƙalubalen shi ne tabbatar da gaskiya da kuma amfani da kuɗaɗen da aka tara yadda ya kamata.

Okereke ta ce abin da ta fi mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da cewa alfanun tattalin arzikin sun isa ga dukkan ’yan Najeriya, ciki har da waɗanda ke zaune a ƙauyuka da yankunan karkara.

Ta ce:

“An riga an yi abin da aka yi. Mu faɗa wa kanmu gaskiya. Abin da ke damuna shi ne ina kuɗaɗen tallafin suke tafiya? A nan ne cin hanci da rashawa ke shiga.
“Ba batun tallafin kaɗai ake yi ba, sai dai tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka samu sun amfani dukkan ’yan Najeriya.”

Kara karanta wannan

'Ba a cire sunan Pantami a takara ba': PDP ta kwantar wa masoyanta hankali

An soki tsarin mulkin Tinubu a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tallafin mai: Abin da ya kamata a yi

A cewarta, ya kamata a tabbatar da cewa kowa ya amfana da cire tallafin, ba wasu mutane kaɗan ko wani ɓangare na al’umma kawai ba, cewar Punch.

Da aka tambaye ta ko rashin samun yanayin da take fata bayan hawa mulki zai zama ƙalubale, Okereke ta ce hakan ba zai zama uzuri ba, domin rayuwa tana tattare da ƙalubale.

Ta ce:

“Idan rayuwa ta ba ka lemon tsami, ka yi lemun sha da shi. Kada ka tsaya kan abin da ya riga ya zube; ka yi aiki da abin da kake da shi domin kawo sauyi.”

Rage kudin mai ba dawo da tallafi ba ne

An ji cewa kamfanin NNPCL ya ce ya fara rangwamen Naira 66 kan kowace litar fetur tun ranar 1 ga Oktoba, domin bikin cikar Najeriya shekaru 66.

Kamfanin ya bayyana cewa rangwamen zai ci gaba har zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2026, kuma manufarsa ita ce rage wa ’yan Najeriya radadin tsadar man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.