ADC Ta Kawar da Shakku, Ta Bayyana Wurin Kaddamar da Kamfen din Atiku a Sokoto

ADC Ta Kawar da Shakku, Ta Bayyana Wurin Kaddamar da Kamfen din Atiku a Sokoto

  • Jam'iyyar ADC mai adawa ta bayyana wurin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta na shugaban kasa a jihar Sokoto
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai isa filin jirgin saman Sultan Abubakar III da misalin ƙarfe 9:00 na safe
  • Sanata Ibrahim Lamido ya buƙaci shugabannin jam’iyyar a ƙananan hukumomi 23 da sauran ƙungiyoyin magoya baya su tabbatar da halartar taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Jam’iyyar ADC ta bayyana wurin da za ta gudanar da bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Sanata Ibrahim Lamido, mai kula da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar a Jihar Sakkwato, ya bayyana cewa za a gudanar da taron ne a sakatariyar ADC da ke kan titin Ilorin, a cikin birnin Sakkwato, ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

Duk da zargin barazana, Atiku zai kaddamar da yakin neman zabensa a Sokoto

ADC za ta yi taro a Sokoto
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Lamido ya ce manyan baƙi da mambobin jam’iyyar sun fara shirye-shiryen gudanar da taron, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Dalilin ɓoye wurin taron a baya

Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar adawar ta ƙi bayyana wurin da za ta gudanar da taron farko na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa saboda zargin barazana da kuma yunƙurin hana ta gudanar da ayyukanta.

Dan takarar gwamnan ADC a Sokoto, Hon. Manir Muhammad Dan’iya, ya tsira ba tare da rauni ba bayan wasu ’yan bindiga sun buɗe wuta kan ayarinsa.

Lamarin ya faru ne a kusa da filin jirgin saman Sultan Abubakar III da ke Sokoto a daren ranar Juma’a. Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta musanta zargin cewa tana da hannu a harin.

Haka kuma, bayan kwana uku da faruwar lamarin, an rufe wani ofishin yaƙin neman zaɓen ADC a jihar.

An kuma yi zargin cewa gwamnatin Jihar Sokoto ta hana jam’iyyar samun wani wuri da ya dace domin gudanar da taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta.

Kara karanta wannan

ADC na neman darewa saboda takarar Atiku a 2027? An ji yadda zancen yake

Atiku ya zargi APC da DSS da shirin hana taron

A daren ranar Talata, tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa APC da DSS na shirin kawo cikas ga taron farko na yaƙin neman zaɓen jam’iyyar. Sai dai DSS ta musanta zargin da Atiku ya yi.

A cikin sanarwar da ya fitar, Lamido ya ce ana sa ran Atiku zai isa filin jirgin saman Sultan Abubakar III da ke Sakkwato da ƙarfe 9:00 na safe.

Ya gayyaci mambobin jam’iyyar da sauran al’umma da su tarbi tsohon mataimakin shugaban ƙasar a filin jirgin saman kafin su wuce zuwa wurin taron da ke lamba 1, titin Ilorin, Sokoto.

ADC ta buƙaci magoya baya su halarci taron

Sanarwar ta kuma buƙaci shugabannin jam’iyyar a dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar da kuma shugabannin mazabu su fara shirye-shiryen tattara magoya baya.

Haka kuma, Lamido ya buƙaci masu kula da harkokin wayar da kan jama’a, ƙungiyoyin goyon baya, ƙungiyoyin mata da na matasa su yi amfani da tsarin da suke da shi domin tabbatar da halartar jama’a da dama.

Kara karanta wannan

El Rufai ya aiko sako ga masoya da magoya baya kan 'yan takarar da za su zaba a 2027

Jam’iyyar na fatan samun halartar mambobinta da magoya bayanta daga sassa daban-daban na jihar domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar.

ADC za ta yi taro a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An rufe ofishin ADC a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta rufe daya daga cikin ofisoshin jam’iyyar ADC mai adawa sakamakon takaddamar mallakar ginin da ke cikinsa.

Gwamnati ta ce ta dauki matakin ne domin kare rayuka da dukiyoyi, bayan wani rikici da ya barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar da wasu bata-gari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng