Tashin Hankali: An Farmaki Magoya Bayan Dan Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2027
- Rahotanni sun nuna cewa wasu mahara da ake zargin ’yan daba ne sun kai wa magoya bayan jam’iyyar NDC hari a Asaba jihar Delta
- Injiniya Thompson Omoneje ya ce maharan sun fasa gilashin motar magoya bayan tare da lalata wasu sassa
- Gwamnatin Delta ta umarci jami’an tsaro su binciki rikicin siyasa tare da gurfanar da duk wanda aka samu da laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta, Nigeria - An ahiga tashin hankali a ranar Asabar a Asaba, babban birnin jihar Delta, bayan zargin kai hari kan magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi.
An ruwaito cewa wasu yan daba da ake zargin suna da alaka da jam'iyyar APC mai mulki ne suka kai hari kan magoya bayan Peter Obi.

Source: Facebook
A rahoton Leadership, Injiniya Thompson Omoneje, wani kodineta a NDC, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da magoya bayan jam’iyyar suka fito tattaki domin nuna goyon baya ga ɗan takararsu na shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso
Yadda aka farmaki magoya bayan Obi
Omoneje ya yi zargin cewa maharan, waɗanda suka sanya baƙaƙen kaya kuma suka iso cikin babura masu kafa uku (Keke Napep), sun tunkari magoya bayan tare da lalata motocinsu.
Ya yi ikirarin cewa waɗanda ake zargin maharan ne, waɗanda ake dangantawa da masu sana’ar tuka Keke a yankin COMATOA da ke Asaba, sun yi wa mutanen da ke cikin wata mota kwanton bauna kafin su kai musu hari.
A cewarsa, maharan sun fasa gilashin gaban motar tare da lalata wasu sassanta.
Omoneje ya nuna damuwa kan lamarin, wanda ya sake jawo tambayoyi game da tsaron magoya bayan ’yan siyasa da kuma buƙatar juriya tsakanin ƙungiyoyin siyasa, musamman a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ƙamari.
"Wannan lamari ya nuna buƙatar ’yan siyasa da magoya bayansu su rungumi tattaunawa cikin lumana, su mutunta ra’ayoyin siyasa da suka bambanta da nasu, tare da kauce wa duk wani mataki da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a," in ji shi.

Kara karanta wannan
Kare ya haddasa babbar matsala da ake zargin ta jawo kashe wani bawan Allah a Kano
Gwamnatin Delta ta dauki mataki
Gwamnatin jihar Delta ta umarci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a wani rikicin siyasa tsakanin wasu da ake zargin magoya bayan NDC da APC ne a Effurun.
Kwamishinan ayyuka na jihar kuma mai yaɗa bayanai, Charles Aniagwu, ya ce Gwamna Sheriff Oborevwori ya umarci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Ya jaddada cewa bai kamata a bar hamayyar siyasa ta rikide zuwa daba ko tsoratar da mutane ba.
Aniagwu ya buƙaci magoya bayan jam’iyyun gwamnati da na adawa su bi doka, yana mai cewa fafatawar siyasa bai kamata ta zama takarar nuna ƙarfin tuwo ba.
Yan daba sun jefi ayarin Peter Obi
Kun ji cewa an kai wa ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, hari a Calabar, jihar Cross River.
Harin ya faru ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani otal da ke gaban filin wasa na U.J. Esuene, bayan ziyarar girmamawa da suka kai wa Obong na Calabar.
Asali: Legit.ng