Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Muhimmin Sako ga Masu Son Samun Tallafin N50,000

Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Muhimmin Sako ga Masu Son Samun Tallafin N50,000

  • Gwamnatin Tarayya ta ce ana zabar wadanda za su amfana da tallafin N50,000 na wata-wata ta hanyar tsarin kwamfuta kai tsaye
  • Ma’aikatar Harkokin Jin Kai ta ce babu bukatar cike fom, biyan kudi ko neman alaka da jami’an gwamnati ko yan aiyasa domin samun tallafin
  • Gwamnati ta gargadi jama’a kan masu neman kudi ko alkawarin taimaka musu wajen samun gurbi a shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya – Gwamnatin Tarayya ta bayyana ta sake yin bayani ga yan Najeriya, wadanda suka samu da ma wadanda ba su samu tallafin N50,000 da aka fara turawa ba.

Gwamnatin ta sake nanata cewa ana zabar wadanda za su amfana da tallafin N50,000 na wata-wata karkashin shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI) ne ta hanyar tsarin kwamfuta mai sarrafa kansa.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Matashin da ya auri mata 2 rana 1 ya rasu a wani yanayi mai cike da al'ajabi

Bernard Doro.
Ministan harkokin jin kai da yaki da talauci, Dr. Bernard M. Doro a ofishinsa da ke Abuja Hoto: Dr. Bernard M. Doro
Source: Facebook

A ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamba, 2026, Ma’aikatar Harkokin Jin Kai ta Tarayya, karkashin jagorancin Bernard Doro, ta yi wannan karin haske a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.

Legit.ng ta ruwaito cewa ma’aikatar ta fitar da bayanin ne yayin da take amsa tambayoyin jama’a kan yadda shirin tallafin ke aiki.

Al’ummar Najeriya, kasa mafi yawan jama’a a Afirka, na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki sakamakon hauhawar farashin kayan abinci, karin kudin makamashi da tsadar rayuwa,.

Wannan yanayi ya kara nuna bukatar shugabannin gwamnati su samar da tallafi mai ma’ana ga ‘yan kasa da ke kokarin biyan bukatun yau da kullum.

Sako ga masu son samun tallafin

Ma’aikatar ta bayyana cewa babu bukatar ‘yan Najeriya su cike wani fom, su biya kudi ko su nemi alaka da jami’an gwamnati domin samun tallafin.

A sakon da ta wallafa, ma’aikatar ta ce:

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta yi bayani kan shafukan da mutum zai shiga domin samun tallafin N50,000

“Ma’aikatar ta yi karin bayani kan tambayoyin da ake yawan yi game da tallafin N50,000 na NERSI. Ana zabar wadanda za su amfana ta hanyar tsarin kwamfuta mai sarrafa kansa; babu bukatar neman tallafi, biyan kudi ko amfani da wata alaka ta musamman.”

Bayanin ma’aikatar ya kuma zama gargadi ga jama’a. Ma’ana, duk wanda ya tuntubi mutane yana alkawarin samar musu da gurbi a shirin a madadin kudi ko wata alfarma, ya kamata a yi taka-tsantsan da shi.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin tarayya Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Ina ake samun sahihan bayanai?

Ma’aikatar ta bukaci ‘yan Najeriya da su rika samun sahihan bayanai kan shirin NERSI daga shafukanta na Facebook da X.

Hukumomin sun kuma shawarci jama’a da su ziyarci shafin yanar gizon ma’aikatar mai adireshin fmhapr.gov.ng domin samun sabbin bayanai kan shirin.

Da gaske an fara cike tallafin N50,000?

Kun ji cewa Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan shirin tallafin N50,000 yayin da aka fara yada wasu shafukan yanar gizo na damfara.

Ma’aikatar jin kai ta ce tallafin N50,000 na musamman ne ga talakawa da gidajen da ke cikin mawuyacin hali sakamakon tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262