Malamin da Aka Cire a Limanci saboda Goyon Bayan Tinubu Ya Lashe Amansa

Malamin da Aka Cire a Limanci saboda Goyon Bayan Tinubu Ya Lashe Amansa

  • Malam Danmalam na Bauchi ya nemi afuwar al'umma kan ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan zargin goyon bayan Tinubu a 2027
  • Limamin ya zargi kafafen yaɗa labarai da karkatar da kalamansa tare da ƙara girman masallacin da yake jagoranta
  • Ya bayyana cewa mutum bakwai ne kawai ke cikin jama'arsa, yana mai cewa sun warware matsalar cire shi daga mukaminsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Wani limami a jihar Bauchi, Dahiru Abubakar, wanda aka fi sani da Malam Danmalam, ya nemi afuwar al'umma bayan ce-ce-ku-ce

Limamin ya nemi afuwar ne bayan rahotannin cewa an cire shi daga mukaminsa na babban limamin unguwar Madina da ke Bauchi saboda goyon bayan sake zaɓen Tinubu a 2027.

Limami ya ba da hakuri
Dahiru Abubakar DanMalam da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Gaskiya TV.
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya ce cire limamin ya tayar da kura a tsakanin al'umma, inda wasu suka zarge shi da neman kusanci da 'yan siyasa, yayin da wasu suka yi tambaya kan sahihancin mukamin da yake riƙe da shi.

Kara karanta wannan

Sama da kasa ba za su hade ba idan aka hana Atiku takara in ji ministan Tinubu

An gayyaci DanMalam hukumar Hisbah

Lamarin ya kai ga hukumar Shari'a ta jihar Bauchi, wadda ta gayyaci limamin domin ya yi bayani kan kalaman da ya yi.

A yayin ganawar da Malam Muhammad Muhammad Bununu, kwamandan Hisbah na hukumar, ya jagoranta, Dahiru ya samu damar bayyana matsayarsa kan zargin da ake yi masa.

Limamin ya zargi kafafen yaɗa labarai da karkatar da kalamansa tare da ƙara girman masallacin da ake magana a kai.

Ya ce:

“Na yi wannan furuci, amma ban yi tsammanin zai jawo irin wannan ce-ce-ku-ce ba. Masallacin da ake magana a kai ba shi da layukan sallah sama da biyu. Ƙaramin masallaci ne, ba masallacin Juma'a ba.”

Ya ƙara da cewa wasu mutane a faɗin duniya sun fahimci masallacin a matsayin babban masallacin Juma'a, alhali kuwa ba haka yake ba.

An cire liman a jan salla saboda Tinubu
Taswirar jihar Bauchi da jam'iyyar APM ke mulki. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da DanMalam ke nufi

Dahiru ya bayyana cewa siyasa ce ta sa aka karkatar da ma'anar kalamansa, yana mai cewa: “Ban taɓa cewa masallacin Juma'a ba ne. Ƙaramin masallaci ne. Bai kamata a faɗaɗa lamarin har ya kai ga ɓata sunan wasu gwamnatoci ba.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda ya yi tukin tasi domin rufa wa kansa asiri a Amurka

Ya kuma nemi afuwar duk wanda ya fahimci kalamansa ba daidai ba, musamman waɗanda suka ɗauka cewa yana magana ne kan babban masallacin Juma'a.

A cewarsa:

“Ina neman afuwar duk wanda ya fahimci cewa masallacin Juma'a nake magana a kai. Ba haka nake nufi ba. Ƙaramin masallaci nake magana a kai.”

Limamin ya kuma bayyana cewa mutum bakwai ne kawai ke cikin jama'ar da yake jagoranta, yana mai cewa sun riga sun warware duk wata matsala da ta taso tsakaninsu kan batun cire shi daga mukaminsa.

Dalilin cire limamin a Bauchi

Mun ba ku labarin cewa an cire Imam Dahiru Abubakar daga limanci bayan zargin yaƙin neman zaɓen Tinubu a lokacin wa’azi bayan salloli.

Kwamitin masallacin ya bayyana cewa ya sha gargaɗin limamin kan mayar da masallaci dandalin siyasa.

Ana zargin limamin ya kuma nemi a sauya sunan masallacin zuwa “Masjid Imam Bola Ahmed Tinubu”, amma kwamitin ya ƙi amincewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.