Rasha za Ta Sayar wa Iran Manyan Makamai yayin da Trump ke Mata Barazana

Rasha za Ta Sayar wa Iran Manyan Makamai yayin da Trump ke Mata Barazana

  • Rahotanni sun nuna cewa Rasha ta amince ta samar wa Iran da na’urorin harba makamai masu linzami guda 90 a yarjejeniyar da suka kulla a 2024
  • Yarjejeniyar na ƙara nuna yadda dangantakar soji tsakanin Moscow da Tehran ke ƙara ƙarfi duk da matsin lambar ƙasashen Yamma
  • Rahoton ya fito ne bayan wani babban jami’in tsaron Iran ya ziyarci Shugaba Vladimir Putin domin tattauna faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Rasha – Rahotanni sun bayyana cewa Rasha ta amince ta sayar wa Iran da na’urorin harba makamai masu linzami guda 90 masu inganci, a wani mataki da ke nuna zurfafa dangantakar soji tsakanin ƙasashen biyu.

Rahoton ya fito ne kwana guda bayan wani babban jami’in tsaron Iran ya ziyarci Moscow domin tattauna faɗaɗa yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen biyu suka rattaba wa hannu a bara.

Kara karanta wannan

Zabe ya wuce, Trump na shirin kaddamar da manyan hare hare Iran

Masoud Pezeshkian da Vladimir Putin
Masoud Pezeshkian da Vladimir Putin a Rasha. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Financial Times ce ta wallafa rahoton a ranar Juma'a, bisa wasu takardun wani babban kamfanin kera makamai na Rasha.

Yadda makaman suke aiki

Rahoton ya bayyana cewa na’urorin da Rasha ta amince za ta samar wa Iran an ƙera su ne domin harba wani makamin linzami mai sarrafa kansa da ake kira LMUR ko Izdeliye 305.

Makamin na iya kai hari kan wuraren da ke motsi, kuma an fara amfani da shi a aikin soji a shekarar 2022. Tun daga lokacin, sojojin Rasha sun yi amfani da shi sosai a yaƙin da suke yi a Ukraine.

Al Jzeera ta rahoto cewa an ƙera makaman ne domin jiragen yaƙi masu saukar ungulu na Mi-28, waɗanda Iran ta riga ta mallaka.

Sai dai rahoton ya ce ba a tabbatar da cewa an kai wa Iran makaman da na’urorin harba su ba.

Karfin dangantakar Rasha da Iran

Yarjejeniyar ta nuna yadda haɗin gwiwar soji tsakanin Moscow da Tehran ke ƙaruwa tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da cikakken farmakinta kan Ukraine a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Shugaban Paraguay ya yi murabus saboda gaza shawo kan matsalolin jama'ar shi

Jami’an leƙen asirin ƙasashen Yamma sun yi gargaɗin cewa dangantakar ƙasashen biyu ta ƙara ƙarfi a yayin yaƙin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Wannan na zuwa ne duk da iƙirarin Shugaba Donald Trump na baya-bayan nan cewa Rasha ba ta bayar da wani gagarumin taimako ga Iran.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump zai shiga jirgi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A ranar Alhamis, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya gana da babban jami’in tsaron Iran, Mohsen Rezaei, a fadar Kremlin.

Rezaei ya kai wa Putin saƙo daga Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei. Fadar Kremlin ta ce ziyarar ta kasance domin ƙara bunƙasa haɗin gwiwar ƙasashen biyu.

An so kashe Trump a Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami’an tsaron Amurka sun kama wani mutum dauke da bindigogi kusa da fadar White House bisa zargin yin barazanar kashe Shugaba Donald Trump.

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta bayyana cewa wanda ake zargin yana cikin wata motar sata, inda jami’an tsaro suka gano bindigar AK da wasu bindigogi biyu tare da harsasai.

Rahoton ya ce mutumin dan kasar Venezuela ya shaida wa jami’an tsaro cewa wasu muryoyi ne suka umarce shi da ya je Washington domin kashe Trump.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng