"Makomar Matasan Najeriya Ta Dogara da Wanda Za Su Zaɓa a Babban Zaben 2027"
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce makomar matasan Nijeriya ta dogara da sakamakon babban zaben 2027
- Tinubu ya bukaci wadanda suka yi rajistar zabe su je su karbi katin PVC dinsu gabanin zaben da ke tafe
- Shugaban ya ce gwamnatinsa na kokarin biyan basussukan fansho da alawus-alawus na ma’aikatan da suka yi ritaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers, Nigeria - Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci matasan kasar da su taka rawar gani a babban zaben shekarar 2027, yana mai cewa sakamakon zaben zai yi matukar tasiri ga makomarsu.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wajen gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Rivers ranar Asabar.

Source: Facebook
Shugaban kasar ya ce matasa na da alhakin taimakawa wajen tsara makomar Nijeriya ta hanyar shiga harkokin zabe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan
“Ko zai shafi Tinubu a 2027?” Yadda al’ummar Legas suka tarbi Kwankwaso ya ja hankali
Tinubu ya bayyana makomar matasa
Tinubu ya bayyana cewa zaben mai zuwa ya shafi matasa ne kai tsaye, inda ya jaddada cewa makomarsu za ta dogara da sakamakon zaben 2027.
“Ya ku matasan Nijeriya, ina kallonku. Wannan zabe naku ne, ba nawa ba. Makomarku ta dogara da wannan zabe,” in ji shi.
Ya kuma bukaci wadanda suka yi rajistar zabe amma ba su karbi katin zabe (PVC) ba da su je cibiyoyin karbar katuna da suka dace domin karbarsa.
Shugaban kasar ya bayyana katin PVC a matsayin muhimmin makamin da ‘yan kasa za su yi amfani da shi wajen zabar shugabannin da za su tafiyar da kasar.
Ya roki matasa da kada su yi watsi da damar da suke da ita ta shiga zabe, yana mai cewa kuri’unsu za su ba su damar bayyana ra’ayinsu kan alkiblar da suke son kasar ta bi.
“Ya rage gare ku ku yi amfani da makamin da kuke da shi. Wannan makami kuwa shi ne katin PVC. Idan ba ku karbi naku ba, don Allah ku je ku karba. Ina rokonku dan girman Allah,” in ji Tinubu.
Tinubu ya tabo batun manufofinsa
Shugaban kasar ya kuma yi karin haske kan manufofin tattalin arzikin gwamnatinsa, inda ya ce bunkasa tattalin arziki da raba arzikin kasa na da muhimmanci wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, musamman matasa.
Ya ce gwamnatinsa na kokarin biyan wasu basussukan da gwamnatocin baya suka bari, ciki har da kudaden fansho da alawus-alawus da ake bin tsoffin ma’aikatan gwamnati.

Source: Facebook
A cewarsa, an tara basussukan fansho da alawus-alawus da yawansu ya kai biliyoyin da tiriliyoyin Naira kafin hawansa mulki, amma gwamnatinsa na kokarin biyan kudaden da ake bin wadanda abin ya shafa.
Tinubu ya tuna rayuwarsa a Akwa Ibom
Kun ji cewa Shugaban Najeriya, Bola Tinubu , ya tuna farkon lokacin da ya yi aiki a Jihar Akwa Ibom, inda ya kasance mai binciken kudi na kamfanin Mobil.
Ya ce bai taba tunanin cewa wata rana zai zama shugaban kasa, sannan ya dawo jihar Akwa Ibom domin kaddamar da filin jirgin sama da aka sanya wa sunan wani tsohon abokin aikinsa, Victor Attah ba.
Asali: Legit.ng
