Wike Ya Bayyana Mutumin da Ya Yi Silar Hawan Shi Kujerar Gwamna a Rivers
- Nyesom Wike ya shaida wa duniya irin taimakon da Daniel Orbih ya yi masa a fagen siyasa a shekarun baya
- Ministan na Abuja ya ce akwai hannun marigayin wajen zaman sa gwamnan jihar Rivers a jam'iyyar PDP
- Wike ya yi maganar ne yayin da ake tuna wa da ‘dan siyasar da ya mutu a karshen Agustan shekarar bana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ministan Harkokin Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ya tuna yadda Daniel Orbih ya taimake shi a siyasa.
Nyesom Wike ya ce marigayi jigon na jam'iyyar PDP, Daniel Orbih, ya goyi bayan neman takararsa ta gwamnan Rivers.

Source: Facebook
Dan Orbih ya taimaka wa Nyesom Wike
Hukumar dillacin labarai wato NAN ta rahoto shi yana bayanin yadda Orbih ya tsaya masa a 2015 duk da matsin lamba.
Wike ya ce abokan hamayyar siyasa sun yi kokarin su shawo kan marigayin ya janye goyon bayan da yake yi masa a lokacin.
‘Dan siyasar ya yi magana ne a ranar Laraba a wani taron ta’aziyya da tunawa da rayuwar Orbih da aka gudanar a Abuja.
"Yau ni Ministan Abuja ne; jiya ni gwamna ne. Wane ne Ubangiji Ya yi amfani da shi domin in zama gwamna? Dan ne,"
- in ji Wike.
Wike ya ce abin duniya bai rudi Orbih ba
A cewar Wike, an sha matsa wa Orbih lamba sosai a lokacin da ake shirin takara a 2015, aka yi masa tayin abin duniya.
Yake cewa duk da wannan, marigayin ya tsaya tsayin-daka har sai da ya ga ya gaji Rotimi Amaechi a gidan gwamnatin Rivers.
Ya ce:
Gwamnana na lokacin ya aika mutane wurin Dan Orbih, suka ba shi komai na duniya, amma Dan ya tsaya kyam ya ce, 'A'a, ba zan karba ba, ba zan amince ba,'"
Orbih ya ba Wike kyautar motoci ana kamfe
Wike ya ce gudumuwar ba ta tsaya ga fitowa fili ya goyi bayan burinsa ba, ya hada da kyautar motoci marasa jin harasahi.
Duk da wadannan Mercedes-Benz da ya kashe lokacin yakin neman zabensa, Wike ya ce Orbih bai nemi a ba shi komai ba.

Kara karanta wannan
Maganar zargin Dickson na shirya wa Obi da Kwankwaso makarkashiya ta yi nisa a NDC
Tribune ta ce ministan Abujan ya tuno yadda tsohon shugaban na PDP ya nemo masa goyon bayan jama’an Kudu maso Kudu.
"Dan ba dan siyasar Najeriya na yau da kullum ba ne. A tsawon shekaruna takwas a matsayin gwamna, bai taba zuwa ko rana daya ba, ko ta waya ko ta zuwa gidana, ya ce, 'ina bukatar wannan kwangilar' ko sau daya ba.
Manyan 'yan siyasa sun tuna da rayuwar marigayin
Ban da Rivers, Wike ya yabi marigayin game da gudumuwar da ya bayar wajen samar da hadin kai a siyasar mahaifarsa, Edo.
Saboda haka ne ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar Edo da su girmama marigayin da jana'izar da ta dace da irin shi.
Irinsu Adams Oshiomhole da Magnus Abe tuna da Dan Orbih, wanda ya rasu a ranar 31 ga watan Agusta yana shekara 64 a duniya.

Source: Facebook
An dawo da abin da aka yi a 1967
Rahoton nan ya ce Gwamnatin Tarayya ta shirya yin shelar neman afuwa game da kisan kiyashin da aka yi Asaba lokacin yaki.
Za a fitar da sanarwa a hukumance ta sasantawa bayan shekaru 59 da faruwar lamarin sa'ilin da kasar ta barke da rikicin basasa.
Gwamnan Delta ya bukaci amincewa da laifin da aka yi wa mutanensu lokacin da mutanen biyafara suka nemi su bar kasar.
Asali: Legit.ng

