Amaechi Zai Iya Samun Kan Shi a Matsala saboda Kalaman da Ya Yi game da APC
- Nyesom Wike ya bukaci INEC ta hukunta Rotimi Amaechi kan kiran masu zaben Tinubu a 2027 mahaukata
- Ministan na Abuja Ya ce irin wadannan kalamai na iya tunzura jama’a kuma ba su dace da yakin neman zabe ba
- Wike ya kuma soki INEC da kafafen yada labarai kan yadda suke tafiyar da lamarin ba tare da daukar mataki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ya yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa.
Nyesom Wike yana so INEC ta dauki mataki kan Rotimi Amaechi saboda kalaman da ya yi kan ‘yan APC da Bola Tinubu.

Source: Facebook
Kalaman Rotimi Amaechi sun tada kura
VON ta ce Wike ya tabo zancen ne da yake magana a ranar Juma’a, bayan ganawa da shugabannin kananan hukumomi.
Mista Wike ya bayyana kalaman da Amaechi ya yi a garin Edo a matsayin na rashin tunani kuma masu tunzura jama’a.
Amaechi, wanda yake dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC ya ce mahaukata ne kawai za su zabi Tinubu a 2027.
Nyesom Wike yana so a hukunta RotimI Amaechi
Wike ya ce ya kamata hukumomi su gudanar da aikinsu yadda ya kamata, yana so a hukunta tsohon mai gidansa a siyasa.
Ministan ya nuna rashin jin dadinsa kan abin da ya kira gazawar hukumomin da suka dace su dauki mataki kan kalaman nan.
Ya ce bai kamata a kyale irin wannan hali ba tare da daukar wani mataki ba.
An rahoto shi yana cewa:
“Har yanzu ban ji cewa INEC ta kira hankalin Amaechi kan wadannan kalamai ba.”
Wike ya ce duk sun ga yadda Amaechi ya bayyana a talabijin yana cewa barayi da mahaukata ne kawai za su zabi Shugaba Tinubu.
Ya kara da cewa Amaechi ya kuma yi ikirarin idan mutanen jihar Edo suka zabi Tinubu, hakan yana nufin su ma mahaukata ne.
Ministan ya bayyana cewa abin mamaki ne yadda ‘dan takara zai yi amfani da wadannan kalamai wajen magana da masu zabe.
An yi wa Amaechi barazana da hana shi kamfe
The Cable ta rahoto shi yana gargadin cewa idan Amaechi ya ci gaba da irin haka, zai sha wahala wajen yin kamfe a Ribas.
Ya ce:
“Ba za ka zauna kana kiran masu zabe mahaukata da barayi ba, sannan ka yi tsammanin za ka tsallake ba tare da an dauki mataki a kanka ba.”
Tsohon gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda wasu ‘yan siyasa ke kara amfani da zagi da kalaman da za su tunzura jama’a.
Ya bukaci INEC da ta tabbatar da bin dokokin zabe yadda ya kamata tare da hukunta ‘yan takara da ke maida kamfe tamkar yaki.
A cewarsa, ya kamata ‘yan siyasa su fadi abubuwan da za su yi idan aka zabe su, maimakon cin mutuncin abokan karawarsu.
Yadda Wike ya zama gwamnan Rivers
Ana da labari cewa Nyesom Wike, ya yaba wa marigayi Daniel Orbih na PDP, yana cewa ya tsaya masa a baya har ya zama gwamna.
Marigayin ya dage sai da ya zama gwamnan Ribas a 2015, ba tare da neman wata alfarma ba duk da kudin da ya kashe masa a kamfe
Manyan ‘yan siyasa sun yi jawabin yabo ga marigayin a taron ta’aziyyarsa da aka yi a Abuja watanni bayan ya mutu yana shekara 64.
Asali: Legit.ng


