Bayan Kokarinsa a Rivers, Wike Ya Fadi Jihar da Ya Samar da Gwamna da Kansa
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana yadda ya yi aiki da jam’iyyarsa ta PDP domin taimaka wa Monday Okpebholo na APC
- Wike ya ce ya ƙi goyon bayan Asue Ighodalo duk da cancantarsa, saboda bai son tsohon gwamna Godwin Obaseki ya sake samun iko
- Ya bayyana cewa ƙungiyar Rainbow Coalition za ta haɗa kan ’yan APC da PDP domin tallafa wa Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana yadda ya taimakawa gwamna ya ci zabe.
Wike ya ce ya yi aiki a kan jam’iyyarsa ta PDP domin taimaka wa Monday Okpebholo na jam’iyyar APC ya zama gwamnan jihar Edo a zaɓen 2024.

Source: Twitter
Tsohon gwamnan jihar Rivers ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wani taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar Rainbow Coalition a Abuja, cewar Vanguard.
Yadda Wike ya hana Obaseki tasiria Edo
Wike ya ce ƙudurinsa na hana tsohon gwamnan jihar, Godwin Obaseki, zaɓar wanda zai gaje shi ne ya sa ya goyi bayan Okpebholo a kan ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo.
A cewar Wike, Ighodalo ya ziyarce shi fiye da sau uku domin neman goyon bayansa, amma ya ƙi amincewa saboda bambancin ra’ayinsa na siyasa da Obaseki.
Ya jaddada cewa duk da kasancewar Ighodalo ɗan takara mai cancanta, goya masa baya zai zama kamar taimaka wa Obaseki ya ci gaba da riƙe ikon siyasa a jihar.
Wike ya ce:
“Na ce ba zan bari Obaseki ya samar da wanda zai gaje shi ba, duk da cewa ɗan takarar mutum ne mai matuƙar cancanta, wanda ya taɓa zama shugaban banki.”
“Ya zo ganina fiye da sau uku, amma na gaya masa, ‘Ka saurare ni, na san kai ɗan takara ne nagari, amma a wannan zaɓen, ina ba ka haƙuri, domin wannan zaɓe yana tsakaninmu da mutumin da yake goya maka baya, wato Obaseki.
“‘Idan ka yi nasara, zai zama kamar mun dawo da shi kan mulki. Don haka, ina ba ka haƙuri, dole ne ka faɗi zaɓen."

Source: Facebook
Tasirin da kungiyar Rainbow ta yi a Edo
Wike ya ce shigar Rainbow Coalition cikin zaɓen gwamnan Edo ta nuna yadda ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban za su iya haɗa kai domin cimma muradin siyasa ɗaya.
Ya kawo misalin zaɓen Edo ne yayin da yake bayyana dabararsa ta haɗa kan masu ruwa da tsaki na APC da PDP domin tallafa wa Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, cewar Tribune.
Wike ya yi wa Amaechi mummunan fata
Mun ba ku labarin cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi yayin da zabe ke kara kusantowa.
Wike ya yi barazanar cewa za su hana Amaechi kamfen a Rivers idan ya ci gaba da cin mutuncin masu goyon bayan Bola Tinubu.
Ministan ya zargi Amaechi da almundahana da kuɗaɗen jama’a, inda ya ambaci ayyukan asibiti, layin dogo da wutar lantarki daga ciki.
Asali: Legit.ng

