Wike da Gwamnonin adawa sun fito da APC ta fitar da sabon kwamitin yakin zaben Tinubu
- Jam’iyyar APC ta fitar da sabon jerin kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu na 2027, inda aka saka ‘yan adawa
- Nyesom Wike, Ademola Adeleke, Chukwuma Soludo da wasu manyan ’yan siyasa na cikin masu taya APC aikin kamfe
- An sake nada Abdulaziz Yari a matsayin darakta-janar, tare da wasu gwamnoni da manyan ’yan siyasa a kwamitin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Jam’iyyar APC ta fitar da sabon jerin mambobin kwamitin yakin neman zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Najeriya.
Jerin ya kunshi Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike da kuma wasu gwamonin da ke cikin jam’iyyun adawa.
Punch ta ce a jerin akwai Gwamnan Osun, Ademola Adeleke da Gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo na Accord da APGA.
Haka zalika wannan karo an tuna da Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, tsohon gwamnan Legas, Babatunde Fashola.
Haka zalika ba a manta da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo a wannan karo ba.
Bola Tinubu ya rike shugabancin kwamitin kamfe
A sabon jerin da aka bai wa manema labarai a ranar Talata, an nada Shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban kwamitin kamfen a 2027.
Kashim Shettima, da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, za su kasance mataimakan shugabannin kwamitin yakin zaben.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; da Gwamnan Kwara suna mataimakan shugabanni.
Abdulaziz Yari yana nan a matsayin darekta janar
An sake nada Sanata Abdulaziz Yari a matsayin darakta-janar na kwamitin yakin zaben.
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele; Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, na cikin mataimakan darakta-janar.
An kuma nada Sanata Adams Oshiomhole a matsayin mataimakin darakta-janar mai kula da hada kan jama'a domin yakin neman zabe.
Sauran wadanda aka ba mukamai sun hada da Femi Gbajabiamila, wanda zai kula da harkokin gudanarwa; Ibrahim Masari, mai kula da sufuri da ayyuka.
Aminu Masari, mai kula da hada kan 'yan majalisa; da Ministan Ayyuka, David Umahi, wanda zai kula da wayar da kan jama'a kan ayyukan more rayuwa.
James Faleke zai jagoranci shirye-shiryen zabe, daidaita ayyuka, sa ido da kuma hada kan masu ruwa da tsaki.
Sakataren kwamitin kamfen Tinubu bai canza ba
The Cable ta ce an nada Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, a matsayin sakataren kwamitin.
Sanata Ajibola Basiru zai zama mataimakin sakatare, yayin da Hadiza Bala Usman za ta zama mataimakiyar sakataren kwamitin kamfen.
Rahoton da aka samu ya ce kwamitin na APC ya kuma nada masu kula da yakin neman zabe a yankuna shida na siyasar Najeriya.
A Kudu maso Kudu, Gwamna Bassey Otu da Victor Giadom ne aka nada. A Kudu maso Gabas, Gwamnan Enugu, Peter Mbah, da Tjeoma Arodiogbu za su jagoranci ayyukan.
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, da Prince Oladiran Iyantan za su kula da Kudu maso Yamma. A Arewa ta Tsakiya, Muazu Bawa Rijau da Gwamnan Neja, Umar Bago.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, da Garba Datti Muhammad za su kula da Arewa maso Yamma. A Arewa maso Gabas kuwa, tsohon Gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff, da Idris Suhaibu ne za su jagoranci ayyukan.
An ba gwamnoni matsayi a yakin neman zabe
A matakin jihohi, jerin ya kunshi gwamnoni da wasu manyan 'yan siyasa a matsayin masu kula da yakin neman zaben APC a 2027.
Daga cikinsu akwai Ahmadu Fintiri na Adamawa, Umo Eno na Akwa Ibom, Chukwuma Soludo na Anambra, Babagana Zulum na Borno.
Akwai Sheriff Oborevwori na Delta, Hope Uzodimma na Imo, Abba Kabir Yusuf na Kano, Dapo Abiodun na Ogun, Ademola Adeleke na Osun.
A karshe kuma akwai Nyesom Wike a matsayin jagoran Rivers da Babban Birnin Tarayya kamar yadda aka ji tuni har ya ayyana kan shi.
An kuma nada Dauda Lawal a matsayin mai kula da yakin neman zaben a Zamfara.
Kamar yadda jam'iyyar APC ta sanar, kwamitin ya hada da tsofaffin gwamnoni da manyan 'yan siyasa a matsayin masu ba da shawara.
Sun hada da tsofaffin shugabannin APC na kasa, Adebisi Akande da Abdullahi Adamu; tsohon Gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun.
A nan akwai tsohon Gwamnan Osun, Iyiola Omisore; Sanata Ibrahim Dankwambo; Sanata George Akume; Segun Osoba da Wale Edun.
An nada Obafemi George a matsayin mai ba da shawara kan harkokin yada labarai.
Asali: Legit.ng


