"Ko a Mafarki," Tinubu Ya Ce Bai Taba Tunanin Zai Zama Shugaban Kasa a Najeriya ba

"Ko a Mafarki," Tinubu Ya Ce Bai Taba Tunanin Zai Zama Shugaban Kasa a Najeriya ba

  • Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya tuna lokacin da ya yi aiki a jihar Akwa Ibom a matsayin mai binciken kudi na kamfanin Mobil
  • Tinubu ya ce bai taba tunanin zai zama shugaban Najeriya har ya dawo jihar domin kaddamar da filin jirgin sama ba
  • Mai girma shugaban kasa ya yabawa Gwamna Umo Eno kan kammala aikin filin jirgin saman da aka sanya wa sunan Victor Attah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom, Nigeria - Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya tuna farkon lokacin da ya yi aiki a Jihar Akwa Ibom, inda ya kasance mai binciken kudi na kamfanin Mobil.

Tinubu ya tuna wannan lokaci da ya yi aiki a kamfanin Mobil, wanda a yanzu har ya samu damar da ya dawo jihar a matsayin shugaban kasa domin kaddamar da wani filin jirgin sama.

Kara karanta wannan

Sanata Dino Melaye ya jagoranci yi wa Tinubu 'Allah Ya isa' ƙafa 3 a gangamin ADC

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da uwaragidansa, Oluremi Tinubu lokacin kaddamar da filin jirgin sama a Akwa Ibom Hoto: Emmanuel Aqua JP
Source: Facebook

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya bayyana ziyarar da ya kai jihar Akwa Ibom a matsayin komawa gida.

Tinubu bai taba mafarkin zama shugaba ba

Ya ce bai taba tunanin cewa wata rana zai zama shugaban kasa, sannan ya dawo jihar Akwa Ibom domin kaddamar da filin jirgin sama da aka sanya wa sunan wani tsohon abokin aikinsa, Victor Attah.

“Ban taba mafarkin zan zama shugaban kasa ba, har na dawo domin kaddamar da wannan filin jirgin sama da aka sanya wa sunan wani abokin aiki da ya yi wa wannan jiha hidima yadda ya kamata,” in ji shi.

Shugaban kasar ya kuma tuna irin gudummawar da ya bayar wajen bunkasa wasu al’ummomi kamar Ibeno da Eket, inda ya ce dawowarsa jihar ta tuna masa da lokacin da yake aiki a wurin.

“Wannan komawa gida ce a gare ni. Na taba zama a Akwa Ibom a matsayin mai binciken kudi na Mobil. Mun gina Ibeno, mun bunkasa Eket, mun kuma yi abin da ya kamata mu yi,” in ji Tinubu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya bar ƙasar Saudiyya bayan kammala Umrah, an ji birnin da zai sauka

Tinubu ya yabawa Gwamna Umo Eno

Tinubu ya kuma yaba wa gwamnatin jihar bisa mayar da manufofinta zuwa abubuwan da ake iya gani, inda ya bukaci mazauna Akwa Ibom su fahimci muhimmancin ci gaba da kyakkyawan shugabanci.

“Dole ne in yaba tare da amincewa da yadda aka cika buri, tun daga manufa zuwa hangen nesa, sannan daga hangen nesa zuwa aikatawa a wannan gwamnati,” in ji shi.
Shugaba Tinubu
Shugaban kasa, Bola Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima da Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom a wurin kaddamar da aiki Hoto: Emmanuel Aqua
Source: Facebook

Shugaban kasar ya bayyana Gwamna Umo Eno a matsayin mutum mai kyakkyawar zuciya, jajircewa da hangen nesa, tare da yaba masa bisa kammala aikin filin jirgin saman.

“q Umo Eno, gwamna, kai mutum ne mai kyakkyawar zuciya, jajircewa da hangen nesa,” in ji Tinubu.

Tinubu ya kare darajar Naira

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa da ba don sauye-sauyen da ya kawo a harkar musayar kuɗaɗen waje ba, da kuɗin ƙasar ya rasa darajarsa gaba ɗaya.

Shugaban ƙasar ya yi watsi da sukar da ake yi wa gwamnatinsa kan faɗuwar darajar Naira idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262