2027: Kungiya Ta Yi Hasashen Abin da Yake Jiran Takarar Tinubu a Kaduna
- Tinubu/Uba Sani Mobilisation Network ta yi alkawarin ba APC kuri’u miliyan 1.2 a zaben shekarar badi
- Kungiyar magoya bayan na APC ta ce bincike ya sa aka yi wannan hasashe ba kawai lissafin gizo aka yi ba
- Abdulmumini Mohammed Aminu-Zaria ya jero cigaban da Bola Tinubu da Uba Sani suka kawo wa jihar Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Kungiyar Tinubu/Uba Sani Mobilisation Network ta bayyana goyon bayan ta ga tazarcen Bola Tinubu da Uba Sani.
Shugaban Tinubu/Uba Sani Mobilisation Network, Abdulmumini Mohammed Aminu-Zaria ya hango nasarar APC a zaben 2027.

Source: Facebook
A ranar Lahadi Tribune ta rahoto cewa Dr. Abdulmumini Mohammed Aminu-Zaria ya fito yana goyon bayansa ga ‘ya ‘yan APC.
Shugaban kungiyar magoya bayan ya ce shugaban kasa da kuma Gwamnan Kaduna, Uba Sani sun cancanci su zarce kan mulki.
Kuri'u miliyan 1.2 suna jiran Bola Tinubu a Kaduna
A wani taron manema labarai da Aminu-Zaria ya kira a ranar Lahadi, ya ce suna yi wa Tinubu harin kuri’u miliyan 1.2 a 2027.
Tinubu/Uba Sani Mobilisation Network ta ce babu abin da ya sa take tallar Tinubu da Uba Sani illa ayyukan da suka yi wa jama’a.
Meyasa kungiyar take tare da Tinubu/Uba Sani?
Kungiyar ta ce ba alakar siyasa ko biyayya ga jam’iyya ta sa ta tallar shugabannin jam'iyyar APC ba.
“Idan bai yi abin kirki sosai ba, a gaskiya, abin da zan iya yi shi ne in ci gaba da zama abokinsa kuma in bi shi. Duk abin da ya ce, zan bi shi. Amma ba zan bata sunana ba.”
- Aminu Zaria
Aminu-Zaria ya fake da cewa Uba ya jawo cigaba a Kaduna musamman a harkokin abubuwan more rayuwa, tsaro da kiwon lafiya.
Ya kuma ce Tinubu ya mara wa gwamnatin Uba Sani baya wajen yin ayyuka saboda alakar da ke tsakanin jihar da tarayya.

Kara karanta wannan
'Ka mun afuwa': Ɗan Arewa ya roƙi yafiya daga Tinubu bayan watsi da tafiyar Atiku
Aminu Zaria ya ce:
“Da ba don goyon bayan Shugaban kasa ba, da ba a iya cimma wadannan abubuwa ba. Ba za a iya tattauna duk wani ci gaba da aka samu a Jihar Kaduna ba tare da an ambaci Bola Ahmed Tinubu ba.”
An nemi 'yan Kaduna su zabi APC a 2027
The Nation ta rahoto shi yana kira ga mutanen Kaduna su sake zaben Malam Uba domin ya karasa ayyukan da yake yi wa jihar.
Yake cewa shekaru hudu sun yi kadan a kammala ayyukan da aka fara a jihar Kaduna.
“Kira na ga al’ummar Jihar Kaduna shi ne mu ajiye son zuciya a gefe. Idan ya yi abin kirki, mu amince da hakan, sannan mu ba shi damar yin wa’adi na biyu domin ya kammala kyakkyawan aikin da ya fara.”
Cikin ribar da Kaduna ta samu na goyon bayan Tinubu ya ce akwai samun shugaban majalisa, ministoci da kujeru a m’aikatun tarayya.
Ya kuma yi bayanin yadda kiristocin yankin kudancin Kaduna suke tare da gwamnatin APC a yau.

Source: Facebook
Shugaban APC ya kore tafiyar su Wike
Daga baya ake jin labari cewa jam’iyyar APC ta bi bayan gwamnoni a rikinsu da Ministan Abuja, Nyesom Wike da ya kafa wata hadaka.
Nentawe Yilwatda ya ce APC ba za ta goyi bayan ’yan takarar wasu jam’iyyun adawa ba, yana fatali da shirin Rainbow coalition a zaben badi.
Shugaban APC ya nuna za a fito da kansakali domin ganin bayan yunkurin Wike a jihohi domin ganin nasarar jam'iyya mai mulki a ko ina.
Asali: Legit.ng

