An Yi Gamon Katar: Abin da Tinubu Ya Fada wa Fubara bayan APC Ta Hana Shi Takara

An Yi Gamon Katar: Abin da Tinubu Ya Fada wa Fubara bayan APC Ta Hana Shi Takara

  • Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa Gwamna Siminalayi Fubara cewa ba zai yi nadamar amincewa da sasancinsa kan rikicin siyasar Rivers ba
  • Tinubu ya yabawa Fubara bisa balaga, fahimtar juna da mutunta shugabanni, yayin da ya kuma jinjinawa Nyesom Wike kan ayyukan raya ƙasa
  • Gwamna Fubara ya yi alkawarin cewa Rivers za ta samar wa Tinubu ƙuri'u miliyan uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ba Gwamna Siminalayi Fubara tabbaci bayan rikicin siyasar jihar Rivers.

Tinubu ya tabbatar wa Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, cewa ba zai taɓa yin nadamar amincewa da shawararsa ta shiga tsakani kan rikicin siyasar jihar ba.

Tinubu ya kwantar wa Fubara hankali
Shugaba Bola Tinubu da jiga-jigan jam'iyyar APC a taron jihar Rivers. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Yabon da Fubara ya sha daga Tinubu

Kara karanta wannan

Akpabio ya fadi miliyoyin kuri'un da zai samawa Tinubu a 2027

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 7 ga watan Nuwambar 2026, yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a birnin Port Harcourt, cewar Channes TV.

Shugaban ƙasar ya yaba wa Fubara bisa nuna balaga, fahimtar juna da mutunta shugabanni, yana mai cewa gwamnan ya nuna jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce:

"Ina so in gode maka musamman saboda balagarka, fahimtar juna da kuma mutunta hikimar dattawa lokacin da muka shiga tsakani. Ka mutunta matsayarmu kuma ka tabbatar da zaman lafiya. Kai ɗan dimokuraɗiyya ne na gaskiya. Fubara, ba za ka yi nadamar abin da ka yi ba muddin muna raye."
Fubara ya yi wa Tinubu alkawari
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Source: Instagram

Tinubu ya yabawa Nyesom Wike

Shugaba Tinubu ya kuma yabawa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ayyukan raya ababen more rayuwa a Najeriya.

Ya bayyana Wike a matsayin abokin haɗin gwiwar gwamnatinsa wajen aiwatar da ayyukan ci gaba, inda ya bukaci al'ummar Rivers su amince da ƙoƙarinsa.

Kara karanta wannan

An bayyana tulin ayyukan alherin Tinubu a Arewa da ya cancanci tazarce a 2027

Tinubu ya tuna da irin goyon bayan da al'ummar Rivers suka ba shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, yana mai neman sake samun goyon bayansu domin wa'adi na biyu.

Ya yi alkawarin ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da manufofin samar da wadata, cewar rahoton Punch.

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa ta magance matsalolin kuɗaɗen da ta gada, yana mai cewa jihohi 27 daga cikin 36 ba sa iya biyan albashin ma'aikatansu lokacin da ya hau mulki.

Alkawarin kuri'u miliyan uku ga Tinubu

Gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa jihar Rivers za ta samar wa Tinubu kuri'u miliyan uku a zaben shugaban kasa mai zuwa a watan Janairun 2027.

Ya bayyana cewa jam'iyyun APC da PDP na aiki tare a jihar karkashin hadakar siyasa mai kunshe da bangarori daban-daban domin tabbatar da nasarar Tinubu.

Fubara ya kira Wike da mai gidansa

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya buƙaci magoya bayan Rainbow Coalition su daina kiransa shugabansu ko jagora.

Fubara ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da ’yan takarar ƙungiyar a Rivers, inda Wike, ministan Abuja, ya halarta.

Gwamnan ya ce dukkan ɓangarorin siyasar da suka haɗu ƙarƙashin ƙungiyar ya kamata su amince da shugabanci guda, su guji rarrabuwar kawuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.