ADC Ta Samu Tagomashi bayan Hukuncin Kotu da Ya Rusa Takarar Atiku, Shugabanninta

ADC Ta Samu Tagomashi bayan Hukuncin Kotu da Ya Rusa Takarar Atiku, Shugabanninta

  • Ƙungiyar jam’iyyun adawa ta Coalition for Democracy ta yi Allah-wadai da hukuncin kotun da ya tsige shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark
  • Jam’iyyun sun ce matakin na iya zama wani shiri na kawar da sahihan jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027
  • Sun yi kira ga sauran jam’iyyun adawa, ƙungiyoyin farar hula da ‘yan Najeriya su haɗa kai wajen kare dimokuraɗiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

ABUJA – Ƙungiyar jam’iyyun adawa ta Coalition for Democracy, mai ƙunshe da jam’iyyu tara, ta bayyana goyon bayanta ga jam’iyyar ADC bayan kotun tarayya ta soke shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin Sanata David Mark.

Ƙungiyar ta bayyana hukuncin kotun da aka yanke ranar Alhamis a matsayin wani mataki mai haɗari da ka iya zama wani shiri na kawar da sahihan jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotu: Adawa ta kara ƙarfi, jam'iyyun siyasa 9 sun goyi bayan ADC da Atiku

An ci gaba da goyon bayan ADC
Atiku Abubakar da shugabannin ADC a Najeriya. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da Salihu Moh. Lukman ya sanya wa hannu a madadin jam’iyyun, ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa abin da ya faru da ADC a yau na iya faruwa da kowace jam’iyyar adawa a nan gaba, cewar Punch.

Jam'iyyun da ke cikin ƙungiyar Coalition for Democracy

An kafa ƙungiyar Coalition for Democracy ne bayan taron G100 Opposition Summit da aka gudanar a Abuja ranar 31 ga watan Agustan 2026.

Jam’iyyu tara da suka haɗa ƙungiyar sun haɗa da:

1. African Democratic Congress (ADC).

2. Allied Peoples Movement (APM).

3. Democratic Leadership Alliance (DLA).

4. National Rescue Movement (NRM).

5. Nigeria Democratic Congress (NDC).

6. Peoples Democratic Party (PDP).

7. Peoples Redemption Party (PRP).

8. Social Democratic Party (SDP).

9. Youth Progressives Party (YPP).

Ƙungiyar ta bayyana cewa manufarta ita ce kare dimokuraɗiyyar Najeriya, tabbatar da wanzuwar jam’iyyu daban-daban da kuma samar da sahihin zaɓe mai gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Abin da ƴan Kwankwasiyya suka ce da kotu ta rushe takarar su Atiku

Jam’iyyun sun zargi hukumomi da takura wa adawa

Ƙungiyar ta tuna cewa kwana guda kafin hukuncin kotun, ta yi gargaɗi kan yadda ake tauye ’yancin gudanar da harkokin siyasa a Najeriya.

Ta bayyana damuwarta kan hare-haren da ake kai wa magoya bayan jam’iyyun adawa, hana su gudanar da harkokinsu da kuma amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa musu lamba.

A cewar ƙungiyar:

“Idan ana kai wa jam’iyyun adawa hari a kan tituna, ana amfani da hukumomin gwamnati wajen kawo musu cikas, sannan ana barazanar kawar da su ta hanyar hukuncin kotu, ya kamata ’yan Najeriya su tambayi kansu ko har yanzu jam’iyya mai mulki na son fuskantar wata sahihiyar adawa a zaɓe.”

Sun gargaɗi gwamnati kan barazanar dimokuraɗiyya

Ƙungiyar ta ce tana mutunta ’yancin bangaren shari’a da kuma damar waɗanda ba su gamsu da hukunci ba na neman adalci ta hanyoyin da doka ta tanada.

Sai dai ta jaddada cewa bai kamata kotuna su zama hanyoyin da ake amfani da su wajen murƙushe fafatawar siyasa ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: NDC ta dauko da zafi, ta fallasa makarkashiyar da APC ke shirya mata

Ta ce duk wanda ke ƙoƙarin rusa jam’iyyun adawa domin tabbatar da nasararsa, yana barazana ne ga tushen Jamhuriyar Najeriya.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa gwamnati da ba ta iya jurewa adawa ba, ta rasa damar kiran kanta mai bin tsarin dimokuraɗiyya.

Ta kuma yi gargaɗin cewa tauye damar siyasa ga jama’a na iya haifar da mummunan sakamako ga zaman lafiyar ƙasa.

Sun yi kira ga ‘yan Najeriya su kare ADC

Ƙungiyar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga matakin da ADC ta ɗauka na kalubalantar hukuncin kotun ta hanyoyin shari’a da suka dace.

Ta kuma yi kira ga sauran jam’iyyun adawa, ƙungiyoyin farar hula, Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), ƙungiyoyin ƙwadago, kafafen yaɗa labarai da sauran ’yan Najeriya masu kishin ƙasa da su haɗa kai wajen kare tsarin dimokuraɗiyya cikin lumana da bin doka.

A ƙarshe, ƙungiyar ta ce ba za ta zuba ido tana kallon yadda ake mayar da Najeriya ƙasar da ba ta da sahihiyar adawa, zaɓe ba tare da zaɓi na daban ba, ko kuma ƙuri’a ba tare da sahihan zaɓuɓɓuka ba.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya fito ya yi maganganu kan rusa takarar Atiku

Ta jaddada cewa za ta yi adawa da duk wani yunƙuri na murƙushe jam’iyyun adawa tare da sauran masu kishin dimokuraɗiyya.

ADC ta daukaka kara

An ji cewa jam’iyyar ADC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja na ranar 5 ga Nuwamba, 2026, a shari’ar da Nafiu Bala Gombe ya shigar.

ADC ta kuma nemi kotu ta dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an saurari ƙarar da ta ɗaukaka.

Jam’iyyar ta sanar da INEC matakan da ta ɗauka, tare da kira ga mambobinta da magoya bayanta su kwantar da hankalinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.