Abu Ya Girma: Tunani Tinubu Ya Mamaye Zuciyar Minista, Yana zuwa har a cikin Barci
- Ministan harkokin Sbuja, Nyesom Wike ya ce tunaninsa a kullum yana kan yadda yan Najeriya za su sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu
- Tsohon gwamnan ya yi kira ga al’ummar Rivers da su kada wa Tinubu kuri’u masu yawa a babban zaɓen 2027
- Wike ya soki Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Peter Obi, yana mai cewa ’yan adawar ba su da damar ƙalubalantar Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, (FCT), Nyesom Wike, ya ce a kowane lokaci tunaninsa yana kan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.
Wike ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin tarukan tattaunawa da al’ummomin masarautun Rumueme da Apara da ke ƙaramar hukumar Obio-Akpor a Jihar Rivers.

Source: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa tsohon gwamnan Rivers ya ce ya himmatu wajen ganin Tinubu ya samu wa’adi na biyu, inda ya buƙaci al’ummar jihar su fito da yawa su zaɓi shugaban a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Gwamnan Arewa ya je wurin Tinubu, ya fada masa abin da mutanen jiharsa za su yi a zaɓen 2027
Wike na yawan tunanin Tinubu
Wike ya ce hanyar da Tinubu zai bi wajen samun nasara a zaɓen 2027 za ta fi sauƙi fiye da yadda aka yi a zaɓen 2023.
“Idan na kwanta barci, ba tunanin da nke sai yadda za s sake zaɓen shugaban ƙasa, idan abinci nake ci, ina tunanin sake zaɓen shugaban ƙasa. Duk abin da nake yi yanzu ya shafi sake zaɓen shugaban ƙasa ne.
“Mu manta da son zuciya, mu zaɓi wanda ya gane mutanen Jihar Rivers ta hanyar kawo musu ribar dimokuraɗiyya da kuma naɗa ’yan jihar a mukamai daban-daban.
“Na san sake zaɓen Tinubu a 2027 zai fi sauƙi fiye da na 2023. Ya kamata mu nuna godiya ga Tinubu kuma mu tabbatar ya samu kuri’u masu yawa. Za mu iya yin hakan.”
- Nyesom Wike.
Wike ya jero nasarorin Tinubu
Ya ce shugaban ya kawo ayyukan ci gaba da dama a jihar tare da naɗa ’yan asalin Rivers a muƙamai masu muhimmanci a gwamnatinsa, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
'Ka mun afuwa': Ɗan Arewa ya roƙi yafiya daga Tinubu bayan watsi da tafiyar Atiku
Ministan FCT ya kuma soki Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC da abokin takararsa, Rotimi Amaechi, yana zarginsu da yaudarar ’yan Najeriya.
Wike ya ce ’yan siyasar biyu ba su da nagartar da za ta ba su damar ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027, yana ƙara da cewa ADC ba za ta samu mafi ƙarancin kashi 25% na kuri’u a Rivers ba.

Source: Facebook
Wike ya soki Peter Obi
Wike ya kuma soki Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, inda ya bayyana shi da sauran ’yan takarar adawa a matsayin “’yan siyasar da ba za a zaɓa ba”.
Ministan ya shawarci magoya bayansa da abokan siyasarsa a jihar da kada su bari rigingimun cikin gida da saɓanin al’umma su ɗauke hankalinsu.
Wike ya kafa sharadin yin murabus
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana abin da zai saka shi ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Wike ya ce zai sanar da murabus dinsa ranar 17 ga Janairun 2027, idan Tinubu bai samu nasara a Abuja da Rivers ba a zaɓen shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng