An Tunkari INEC kan Rashin Ganin Sunan Pantami da Wasu 'Yan Takara
- Jam’iyyun PDP, NDC, ADC da AA sun fara neman mafita bayan rashin sunayen wasu ’yan takararsu a jerin sunayen da INEC ta fitar na zaben 2027
- Daga cikin ’yan takarar da abin ya shafa akwai Isa Ali Pantami a Gombe, Oladipupo Adebutu a Ogun da Aminu Gwarzo a Kano
- Yayin da wasu jam’iyyun ke zargin an samu kuskuren gudanarwa ko na fasaha, wasu na fuskantar sabani kan tikitin takara da matsalolin shari’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu sun fara daukar matakai domin warware matsalolin rashin sunayen wasu ’yan takara a jerin karshe da INEC ta fitar gabanin babban zaben 2027.
Lamarin ya jawo damuwa da korafe-korafe daga jam’iyyun PDP, NDC, ADC, AA da wasu jam’iyyun siyasa.

Kara karanta wannan
PDP ta shaida matakin da ake dauka game da cire sunayen Pantami da wasu ‘yan takara

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa duk da cewa wasu na zargin kuskuren gudanarwa ko matsalar fasaha, wasu kuma na fuskantar sabani kan shugabanci, takarar jam’iyya da kuma shari’o’in da ba a kammala ba.
PDP ta fara tattaunawa da INEC
Jam’iyyar PDP ta ce ta fara tattaunawa da INEC domin warware rashin sunayen ’yan takararta na gwamna a jihohin Ogun da Gombe.
A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na kasa, Jungudo Mohammed, ya fitar ranar Lahadi, PDP ta ce tana neman mafita cikin lumana bisa doka da ka’idojin zabe.
Jam’iyyar ta bukaci ’yan takarar da abin ya shafa, mambobinta da magoya bayanta su kwantar da hankalinsu, su yi hakuri, tare da guje wa duk wani mataki ko furuci da zai kawo cikas ga tattaunawar da ake yi.
Ladi Adebutu ya yi korafi
Adebutu ya bayyana cewa har yanzu shi cikakken mamba ne mai rijista a PDP, kuma ya cika sharuddan da ake bukata domin tsayawa takarar gwamnan Ogun.

Kara karanta wannan
Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya ce ya kammala rajistar mambobinsa ta yanar gizo a cikin wa’adin da aka kayyade, sannan aka buga katin shaidarsa tare da tantance shi kafin a mika takardun da suka dace ga INEC.
Ya kuma ce an gudanar da zaben fitar da gwani da ya samar da shi a matsayin dan takarar PDP a gaban jami’an INEC da suka halarta a matsayin masu sa ido.
Vanguard ta rahoto cewa Adebutu ya ce:
“Ina sane da damuwar da ta biyo bayan rashin sunana a jerin ’yan takarar gwamnan Ogun na zaben 2027 da INEC ta wallafa. Ina ganin ya dace in yi magana kai tsaye da ku domin tabbatar muku cewa babu abin da zai sa a firgita.”
Maganar da Sheikh Isa Pantami ya yi
A jihar Gombe, bangaren Pantami ma ya bukaci magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, yana mai bayyana rashin sunansa a jerin INEC a matsayin koma-baya na wucin gadi da za a iya warwarewa cikin wa’adin da doka ta tanada.
Pantami ya zama dan takarar gwamnan Gombe na PDP bayan sabon zaben fitar da gwani da aka gudanar ranar 29 ga Satumba, 2026, sakamakon umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar.

Kara karanta wannan
Zaben Gwamna 2027: INEC ta fitar da sunayen ’yan takara 16 a Gombe, babu Pantami a ciki
Kakakin kungiyar Pantamiyya, Farfesa Suleiman Mohammed, ya amince cewa lamarin ya jawo damuwa ga mambobin PDP da magoya bayan Pantami. Sai dai ya ce hakan ba yana nufin an yanke hukunci na karshe kan makomar siyasarsa ba.

Source: Facebook
NDC ta nemi bayani a Kano
A Kano, jam’iyyar NDC ta ce za ta tuntubi INEC domin warware rashin sunan dan takararta na gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, da mataimakinsa, Mustapha Kwankwaso, a jerin sunayen karshe.
Shugaban NDC na jihar Kano, Hussaini Mairiga, ya ce an mika sunayen ’yan takarar ga INEC bisa ka’idojin da suka dace da wa’adin da doka ta kayyade.
A Kaduna ma, sunan dan takarar gwamnan NDC, tsohon Sanata Danjuma Tella La’ah, bai bayyana a jerin ba, a daidai lokacin da ake samun sabani kan tikitin takarar jam’iyyar.
Shugaban NDC na jihar, Evangelist Mordecai Ibrahim, ya danganta rashin sunan da matsala wajen rajistar sunan La’ah.
Ya ce matsalar sadarwa ta intanet a lokacin rajistar yanar gizo ta sa aka yi kokarin rajista fiye da sau daya, lamarin da ya haifar da cakuduwa a bayanan.
AA ta yi barazanar zuwa kotu
Jam’iyyar AA ta yi barazanar kalubalantar rashin sunayen wasu ’yan takararta na gwamna da na majalisun dokoki a jerin INEC.
Shugaban jam’iyyar na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa, Aare Adekunle Omo-Aje, ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da jama’a a Kaduna ranar Lahadi.
Ya ce jam’iyyar na zargin an samu kuskuren fasaha, kuma tawagar lauyoyinta na shirya korafi a hukumance ga INEC domin neman a shigar da sunayen ’yan takarar da abin ya shafa.
Sai dai ba dukkan wadanda aka cire ba ne aka danganta lamarinsu da kuskuren gudanarwa. A Kwara, an cire dan takarar gwamnan AAC, Duwatsu Musa, saboda bai kai shekara 35 da kundin tsarin mulki ya tanada ga masu neman kujerar gwamna ba.
ADC ta yi gargadi kan magudi
A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam’iyyar ADC na kasa, Sanata David Mark, ya yi gargadin cewa jam’iyyar za ta bi ka’idojin zabe, amma ba za ta amince da magudi ba.
Mark ya yi wannan gargadi ne a Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin majalisar gudanarwar Savannah karkashin jagorancin tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola.
Majalisar, wadda aka fi sani da Council of the Wise, ta kai ziyara hedikwatar jam’iyyar ne a matsayin wani bangare na tattaunawarta da jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki gabanin zaben 2027.
Asali: Legit.ng
