Shirin da Atiku da Sauran Yan Adawa ke Yi Na Kawo wa Tinubu Matsala a 2027
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa yana tattaunawa da Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ’yan adawa
- Makinde ya ce tattaunawar da ake yi za ta iya haifar da wata yarjejeniya ta siyasa, da za ta bai wa ’yan adawa dama
- Gwamnan ya bayyana shirin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa idan ya zama shugaban ƙasa, tare da nadin ƙwararrun mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa yana da yakinin ’yan adawa za su cimma yarjejeniyar siyasa.
Makinde ya ce suna shirin ne domin kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da fitaccen mai gabatar da shirye-shirye, Chude Jideonwo da ya wallafa a shafin Facebook.
Makinde ya tabbatar da tattaunar yan adawa
Makinde ya ce manyan ’yan siyasar adawa na ci gaba da tattaunawa kan yadda za su haɗa ƙarfi domin fuskantar jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
A cewarsa, tattaunawar ta shafi yiwuwar haɗa kan masu neman shugabancin ƙasar domin samar da tsayayyar ƙawance da za ta iya ƙalubalantar jam’iyyar mai mulki.
Makinde ya ce:
“Har yanzu muna da damar haɗa kai saboda muna tattaunawa, kuma tattaunawar tana gudana sosai.”
Ya nuna kwarin gwiwar cewa tattaunawar da ake yi za ta haifar da wata yarjejeniya ta siyasa wadda za ta ba ’yan adawa damar fuskantar APC da ƙarfi a zaɓen 2027.
Sai dai ya bayyana cewa ba sa tunanin maimaita tsarin haɗakar jam’iyyun siyasa da aka yi a shekarar 2015, wanda ya haifar da APC tare da kawo ƙarshen mulkin PDP na tsawon shekaru 16.
A cewarsa, bin irin wannan hanya zai zama kamar amfani da dabarar siyasa da Tinubu ya riga ya sani sosai, saboda haka suna nazarin wata hanya ta daban.

Kara karanta wannan
Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur
Gwamnan bai bayyana takamaiman tsarin yarjejeniyar da suke tattaunawa a kai ba, ko kuma ko za a buƙaci wasu daga cikin ’yan takarar shugaban ƙasa su ajiye burinsu domin goyon bayan mutum guda.

Source: UGC
Irin gwamnatin da Makinde ke son kafawa
A yayin tattaunawar, Makinde ya kuma bayyana shirin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta haɗin kan ƙasa idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasa.
Ya ce manufarsa ita ce sake gina Najeriya daga tushe, tare da bai wa ƙwararru damar riƙe muƙamai ba tare da la'akari da siyasa, ƙabila ko yankin da suka fito ba.
Ya ce:
“Abin da muke gabatar wa ’yan Najeriya ta hanyar shirinmu na Reset Agenda shi ne kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta haɗin kan ƙasa. Za a share abubuwan da suka gabata, sannan a kafa ingantaccen tubali.
Makinde ba zai tafi da Tinubu ba
Kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na APM, Seyi Makinde, ya ce ba zai jawo Shugaba Bola Tinubu cikin gwamnatinsa ta haɗin kan ƙasa ba.
Makinde ya zargi Tinubu da rashin cika yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa da suka cimma gabanin zaɓen 2023.
Sai dai ya ce a shirye yake ya naɗa ƙwararrun ’yan APC waɗanda yake ganin za su iya taimakawa wajen tafiyar da gwamnati idan ya ci zaben 2027.
Asali: Legit.ng
