Yayin Kokarin Kifar da Tinubu, ADC Ta Yi Gargadi kan Magudi a 2027

Yayin Kokarin Kifar da Tinubu, ADC Ta Yi Gargadi kan Magudi a 2027

  • Shugaban jam’iyyar ADC, David Mark, ya gargadi masu shirin yin magudi a zaɓen 2027 cewa jam’iyyar ba za ta amince da hakan ba
  • Mark ya ce ADC za ta bi dokokin zaɓe da ƙa’idojinta, amma za ta yi adawa da duk wani yunkurin yin magudin zaɓe ko hana ta shiga takara
  • Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da ya karɓi tawagar Savannah Centre, ƙarƙashin jagorancin tsohon Alƙalin Alƙalai na Najeriya, Olukayode Ariwoola

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban jam’iyyar ADC, Sanata David Mark, ya ce jam’iyyar za ta bi ƙa’idojin zaɓen 2027, amma ba za ta amince a yi mata magudin zaɓe ba.

Mark ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi tawagar Majalisar Gudanarwar Savannah Centre a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Atiku vs Tinubu: Jam'iyyar ADC ta shata layi, ta gindaya sharadi kan babban zaben 2027

Shugaban jam'iyyar ADC
Shugaban ADC, David Mark. Hoto: ADC Vanguard
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa David Mark ya ce ADC za ta mutunta dokokin hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, da kuma ƙa’idodin jam’iyyar.

Mark ya ce jam’iyyar za ta yi siyasa cikin yanayin da zai ƙara wa jama’a amincewa da tsarin dimokuraɗiyya.

Mark ya yi gargadi kan magudi

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya ce ADC za ta yi iya ƙoƙarinta wajen bin ƙa’idojin da aka gindaya, amma ba za ta bari a yi amfani da magudi wajen cire ta daga takarar zaɓen ba.

“Za mu bi ƙa’idoji. Amma ba za mu amince da magudi ba, kuma ba za mu bari a yi mana magudi har a cire mu daga fafatawar zaɓe ba,”

In ji Mark.

Ya ce jam’iyyar tana da niyyar gudanar da siyasa ta hanyar da za ta kare martabar dimokuraɗiyya tare da ƙarfafa amincewar jama’a kan zaɓe.

A baya Mark ya taɓa yin gargaɗi kan amfani da hukumomin gwamnati wajen karkatar da zaɓen 2027, yana mai cewa dole ne a kare sahihancin zaɓen.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya ɗauki zafi, ya ce za a iya kashe duk wanda ya saci akwatin zabe a 2027

Ariwoola ya nemi a guji rikici

Tawagar Savannah Centre, wadda aka fi sani da “Council of the Wise”, ta ziyarci hedikwatar ADC ne a wani ɓangare na tattaunawar da take yi da jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki gabanin zaɓen 2027.

A lokacin ziyarar, Ariwoola ya ce cibiyar na neman tabbacin jam’iyyu da ’yan takararsu cewa za su taimaka wajen ganin an gudanar da zaɓe cikin lumana, ’yanci, adalci da sahihanci.

Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
Atiku Abubakar da abokin takarar shi a ADC. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

This Day ta wallafa cewa ya kuma buƙaci shugabannin ADC su tabbatar da cewa ’yan takararsu da magoya bayansu sun bi dokokin INEC tare da guje wa duk wani hali da ka iya haifar da tashin hankali a lokacin siyasa.

Tawagar da ta ziyarci ADC ta ƙunshi wasu daga cikin mambobin majalisar, ciki har da Farfesa Abdullahi Shehu, Farfesa Azeez Musa Dankano, Ambasada Sani Bala, Tunji Lardner da Ambasada Godswill Ighali.

Cibiyar ta ce tana shirin tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu, shugabannin INEC, jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da malaman addini, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki kafin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban DSS ya hango abin da zai faru da masu shirin magudin zabe a 2027

Ana kamfen din ADC a Gombe

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC a Gombe, Bala Bello Tinka, ya yi alkawarin samar da ilimi kyauta har zuwa matakin jami’a idan aka zaɓe shi.

Tinka ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da mazauna Gombe da magoya bayansa a rangadin da ya gudanar a cikin birnin Gombe da kewaye ranar Talata.

Ya kuma yi alkawarin cire takunkumin hana masu babura masu zaman kansu da 'yan acaba, yin aiki da daddare a birnin Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng