Zaben Gwamna 2027: INEC ta Fitar da Sunayen ’Yan Takara 16 a Gombe, Babu Pantami a Ciki

Zaben Gwamna 2027: INEC ta Fitar da Sunayen ’Yan Takara 16 a Gombe, Babu Pantami a Ciki

  • Hukumar INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamnan jihar Gombe na zaɓen 2027, inda jam’iyyun siyasa 16 suka gabatar da ’yan takara
  • Gwamna Jamil Isyaku na APC, Bala Bello na ADC da Ma’aji Adamu Muhammed na SDP na cikin waɗanda aka amince da su
  • Ibrahim Abubakar Jalo na PRP, mai shekaru 35, shi ne mafi ƙarancin shekaru, yayin da Adeh Nuhu Milah na ADP, mai shekaru 72, shi ne mafi girman shekaru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da cikakken jerin sunayen ’yan takarar da ta amince da su domin fafatawa a zaɓen gwamnan jihar Gombe na shekarar 2027.

Jerin sunayen ya ƙunshi ’yan takara 16 daga jam’iyyun siyasa daban-daban, tare da mataimakansu, shekarunsu, jinsinsu da takardun karatunsu.

Sakatariyar hukumar INEC, Rose Oriaran-Anthony, ce ta sanya hannu kan jerin sunayen, inda shekarun ’yan takarar suka kama daga 35 zuwa 72.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya bayar da shawara ga Pantami da sauran 'yan takarar da INEC ta cire sunayensu

'Yan takarar da za su yi takara a Gombe
Bala da Jamilu | Hotuna; Dr. Jamilu Isyaku Gwamna, Bala Bello Tinka Is Coming
Source: Facebook

APC, ADC, SDP da sauran jam’iyyu sun fitar da ’yan takararsu

Jam’iyyar APC ta tsayar da Gwamna Jamil Isyaku, mai shekaru 60, a matsayin ɗan takararta na gwamna, yayin da Balah Adams, mai shekaru 63, zai yi takarar mataimakin gwamna tare da shi.

Jam’iyyar ADC ta tsayar da Bala Bello, mai shekaru 58, tare da Aliyu Ngolmo Poyilma, mai shekaru 63, a matsayin mataimakinsa.

Haka kuma, SDP ta tsayar da Ma’aji Adamu Muhammed, mai shekaru 58, yayin da Magaji Ibrahim, mai shekaru 64, zai yi takarar mataimakin gwamna.

A jam’iyyar LP kuwa, Muazu Zubairu Halilu, mai shekaru 66, ne ɗan takara, tare da Defle Burga, mai shekaru 61.

Jam’iyyar NNPP ta tsayar da Abdullahi Maikano Umar, mai shekaru 48, tare da Victor Iliya Jatau, mai shekaru 67. NDC kuma ta tsayar da Ardo Babayo Kumo, mai shekaru 62, tare da Umaru Sunday, mai shekaru 43.

Sauran ’yan takarar sun haɗa da Madaki Auwal Haruna, mai shekaru 46, na jam’iyyar AAC.

Kara karanta wannan

Kano: NDC ta yi mamakin cire sunan Gwarzo, ta faɗi tabbacin da INEC ta ba ta

Cikakken jerin sunayen ’yan takarar gwamna 16 a Gombe

Ga jerin sunayen ’yan takarar da INEC ta amince da su da shekarunsu, tare da sunayen mataimakansu a cikin baka:

  1. A: Madaki Auwal Haruna, mai shekaru 46 (Usman Muhammad Adamu, mai shekaru 70).
  2. AAC: Benson Bobo Bagwiba, mai shekaru 38 (Umar Yahaya, mai shekaru 35).
  3. ADC: Bala Bello, mai shekaru 58 (Aliyu Ngolmo Poyilma, mai shekaru 63).
  4. ADP: Adeh Nuhu Milah, mai shekaru 72 (Mohammed Abdullahi, mai shekaru 44).
  5. APC: Gwamna Jamil Isyaku, mai shekaru 60 (Balah Adams, mai shekaru 63).
  6. APM: Lemela Lenos Silas, mai shekaru 67 (Lawan Wadaji Umar, mai shekaru 50).
  7. APP: Yahaya Bappaji, mai shekaru 53 (Adamu Hassan Ibrahim, mai shekaru 35).
  8. DLA: Sani Muhammad, mai shekaru 51 (Samuel Joy, mai shekaru 43).
  9. LP: Muazu Zubairu Halilu, mai shekaru 66 (Defle Burga, mai shekaru 61).
  10. NDC: Ardo Babayo Kumo, mai shekaru 62 (Umaru Sunday, mai shekaru 43).
  11. NDP: Aliyu Adamu Danmacca, mai shekaru 38 (Sulaiman Mariyatu Aliyu, mai shekaru 66).
  12. NNPP: Abdullahi Maikano Umar, mai shekaru 48 (Victor Iliya Jatau, mai shekaru 67).
  13. NRM: Yahya Bashir, mai shekaru 46 (Sulaiman Kumo Mohammed, mai shekaru 56).
  14. PRP: Ibrahim Abubakar Jalo, mai shekaru 35 (Anthony Augustine Maidaka, mai shekaru 41).
  15. SDP: Ma’aji Adamu Muhammed, mai shekaru 58 (Magaji Ibrahim, mai shekaru 64).
  16. ZLP: Gana Aliyu Muhammad, mai shekaru 57 (Garba Abdullahi, mai shekaru 41).

Kara karanta wannan

INEC ta cire sunan Aminu Gwarzo daga jerin 'yan takarar gwamnan jihar Kano a 2027

Jalo na PRP ne mafi ƙarancin shekaru cikin 'yan takarar

A cewar jerin sunayen da INEC ta fitar, Ibrahim Abubakar Jalo na jam’iyyar PRP, mai shekaru 35, shi ne mafi ƙarancin shekaru a cikin ’yan takarar gwamnan jihar Gombe.

A gefe guda, Adeh Nuhu Milah na jam’iyyar ADP, mai shekaru 72, shi ne mafi girma a cikinsu.

Dukkan ’yan takarar gwamna 16 maza ne. Sai dai jerin sunayen ya nuna cewa akwai mata biyu da aka tsayar a matsayin ’yan takarar mataimakin gwamna, wato Samuel Joy, mai shekaru 43, ta jam’iyyar DLA, da Sulaiman Mariyatu Aliyu, mai shekaru 66, ta jam’iyyar NDP.

Haka kuma, babu wani ɗan takara mai nakasa a cikin jerin sunayen da hukumar ta fitar.

PDP ba ta cikin jerin sunayen ’yan takarar Gombe

Sai dai, ba a bayyana dan takarar jam’iyyar PDP ba a cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamnan jihar Gombe na shekarar 2027 da INEC ta fitar ba.

A baya, an samu rikicin cikkin gida a jam'iyyar PDP, inda aka sake gudanar da zaben fitar da gwani a jihar tare da alanta Prof. Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin wanda ya lashe zaben.

Duk da haka, INEC ta gaza bayyana Pantami a matsayin wanda zai yiwa PDP takara a zaben na gwamna da ke tafi farkon shekarar da za mu shiga ta 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng