'Ba a Cire Sunan Pantami a Takara ba': PDP Ta Kwantar wa Masoyanta Hankali
- Jam’iyyar PDP a Gombe ta bukaci mambobinta da magoya bayanta su kwantar da hankula kan jerin sunayen ’yan takarar gwamna
- Jam’iyyar ta nuna damuwa kan cire sunan Farfesa Isa Ali Pantami daga jerin sunayen da ake yadawa, duk da sake zaɓen fitar da gwani
- PDP ta ce tawagar lauyoyinta na aiki da hukumomi domin tabbatar da shigar da sunan Pantami, tare da bin hanyoyin doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Pantami, Gombe - Jam’iyyar PDP reshen jihar Gombe ta yi martani mai zafi bayan rasa sunan Isa Ali Pantami a cikin yan takarar gwamna.
Jam'iyyar ta bukaci mambobinta, magoya bayanta da masu fatan alheri a ciki da wajen jihar su kwantar da hankula kan jerin sunayen ’yan takarar gwamna da ake yadawa.

Source: Facebook
Kakakin jam'iyyar na jihar Gombe, Abdulkadir Ahmad Dukku shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na PDP.
Abin da PDP ke cewa kan takarar Pantami
Jam’iyyar ta ce ta lura da wani jerin sunaye da ake yadawa a kafafen sada zumunta, inda aka ce an cire sunan ɗan takararta na gwamna, Farfesa Isa Ali Pantami.
Ta bayyana cewa ba ta samu wata sanarwa a hukumance daga INEC dangane da lamarin ba.
Jam’iyyar ta nuna damuwa kan rahoton cire sunan Farfesa Pantami, duk da sake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna a ranar 29 ga Satumba, 2026, bisa bin hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe, wanda jami’an INEC suka sanya ido a kansa.
Saboda haka, PDP reshen jihar Gombe ta roƙi INEC da ta mutunta bin doka da oda, tare da sauke nauyin da doka ta ɗora mata a tsarin dimokuraɗiyya, domin tabbatar da adalci, daidaito da gaskiya.

Source: Original
Jan hankali da PDP ta yi a Gombe
Haka kuma, jam’iyyar ta buƙaci mambobinta da magoya bayanta su kwantar da hankula, su tsaya tsayin daka, tare da ci gaba da jajircewa wajen bin tsarin dimokuraɗiyya yayin da suke ci gaba da neman cimma burinsu na siyasa domin al’ummar jihar Gombe.
Bugu da ƙari, jam’iyyar ta yi zargin cewa wasu mutane na ƙoƙarin kawo cikas ga fitowar shugabancin siyasar da take so a jihar.
A halin yanzu, tawagar lauyoyin PDP na aiki kafada da kafada da hukumomin da abin ya shafa da cibiyoyin dimokuraɗiyya domin neman shigar da sunan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a jihar Gombe, bayan sake gudanar da zaɓen fidda gwani a ranar 29 ga Satumba, 2026.
Jam’iyyar ta sake tabbatar wa mambobinta da magoya bayanta cewa ana bin hanyoyin doka da hukumomin da suka dace wajen warware wannan batu.
Dan PDP ya ce akwai haske
Salihi Isa ya ce batun cire sunan Pantami akwai sauran abubuwan da ya kamata mutane su fahimta saboda ba na karshe ba ne.
Ya ce a jira ranar Talata akwai garambawul da za a iya saboda sabon zaben fitar da gwani da PDP ta yi wanda Pantami ya yi nasara.
Pantami ya samu karin goyon baya
A baya, kun ji cewa wasu manyan masu ruwa da tsaki daga Yamaltu/Deba, ciki har da tsofaffin sojoji da ’yan siyasa, sun koma PDP tare da dubban magoya bayansu.
Sababbin ’yan PDP ɗin sun bayyana goyon bayansu ga ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar kuma tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.
Asali: Legit.ng

