Wani Talaka Ya Yi Karfin Hali, Ya Ci Bashin Miliyoyi don Yi wa Tinubu Kamfen

Wani Talaka Ya Yi Karfin Hali, Ya Ci Bashin Miliyoyi don Yi wa Tinubu Kamfen

  • Wani direban karamar mota a Ekiti ya ce ya ciwo bashin Naira miliyan 3.5 domin tallafa wa kamfen ɗin sake zaɓen Bola Tinubu da wasu ’yan siyasa biyu
  • Adeleye Adeniyi ya ce ya ware Naira miliyan 2 ga Tinubu, Naira miliyan 1 ga Opeyemi Bamidele da Naira 500,000 ga Steve Fatoba
  • Direban ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yadda yake ganin ’yan siyasar sun gudanar da mulkinsu bayan nasarar da suka samu a zaben 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ado-Ekiti – Wani direban karamar mota mai suna Adeleye Adeniyi ya bayyana cewa ya ciwo bashin Naira miliyan 3.5 domin tallafa wa sake zaɓen shugaba Bola Tinubu da wasu ’yan siyasa biyu a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tsohuwar gaba ta yi kamari: Wike ya yi wa Amaechi mummunan baki a siyasa

Adeniyi, wanda ya fito daga Ado-Ekiti a Jihar Ekiti, ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai da ake yaɗawa a ranar Juma’a.

Adeleye Adeniyi da Bola Tinubu
Bola Tinubu a hagu da Adeleye Adeniyi a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Damilola Amuda GoalGetter
Source: Facebook

Shafin Damilola Amuda GoalGetter ya fitar da bayanan da mutumin ya yi a bidiyon da ya wallafa a Facebook.

Yadda ya raba bashin kudin

A cewar bayanan da ke jikin cak ɗin, Adeniyi ya ware Naira miliyan 2 domin kamfen ɗin Tinubu, Naira miliyan 1 ga Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, sannan N500,000 ga ɗan Majalisar Dokokin Jihar Ekiti, Steve Fatoba.

Direban ya ce a shirye yake ya fita kamfen domin tallafa wa ’yan siyasar, yana mai cewa ya ɗauki wannan matakin ne saboda yadda yake ganin sun gudanar da ayyukansu.

Motocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Motocin tallata Tinubu a Nasarawa. Hoto: Gov Abdullahi A Sule
Source: Facebook

Ya bayyana cewa yana goyon bayan ƙoƙarin Tinubu na neman wa’adi na biyu, kuma yana son ya yi amfani da kuɗin bashin wajen tallafa masa.

Punch ta wallafa cewa Adeniyi ya kuma ce zai yi amfani da waƙa wajen tallafa wa shugaban, yana mai jaddada cewa a shirye yake ya fita domin neman masa goyon bayan jama’a.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ware gwamna 1 a Arewa, ta yaba masa kan ayyukan alheri

Ya buƙaci a zaɓi Tinubu

Adeniyi ya yi kira ga ’yan Najeriya da su nuna ƙauna ta hanyar sake zaɓen Tinubu, yana mai cewa ya yi imanin shugaban zai kawo ƙarin alherin da jama’a za su amfana da shi idan ya sake samun nasara.

Ya kuma yaba wa Bamidele da Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, kan ayyukan da ya ce suna tallafa wa a fannonin kiwon lafiya, ilimi, wutar lantarki da samar da abubuwan more rayuwa a yankunan karkara.

A cewarsa, ayyukan da Bamidele ke tallafawa suna ƙarfafa masa gwiwa tare da sa shi ganin cewa yana da shugaba nagari.

Ga bidiyon mutumin da News Click ta wallafa a X:

Bwala ya kare Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Daniel Bwala ya yi hasashen cewa shugaban zai samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa na gaba.

Bwala ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya ce yana da yakinin cewa tazarar ƙuri’un da Tinubu zai samu a kan abokan hamayyarsa za ta fi yadda mutane suke tsammani.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Tinubu ya samu ƙuri’u 8,794,726, inda ya doke Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da tazarar ƙuri’u miliyan 1.81.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng