INEC Ta Cire Sunan Dan Takarar Su Kwankwaso a Zaben Gwamnan Jihar Kano na 2027
- Hukumar INEC ta cire sunan ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo, daga jerin sunayen ’yan takarar da ta fitar na karshe
- Jerin sunayen da hukumar INEC ta fitar ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2026, ya ƙunshi ’yan takara 17ciki har da Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Dan tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Abacha Muhammed Sani ne aka saka a jerin a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da sunayen yan takarar gwamnan jihar Kano na karshe da za su kece raini a babban zaben 2027.
INEC ta cire sunan ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, daga cikin jerin sunayen ’yan takarar gwamnan jihar guda 17 da ta fitar.

Source: Facebook
Legit Hausa ta fahimci babu sunan Gwarzo ne a sunayen da INEC ga wallafa a shafinta na yanar gizo ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, 2026.
Kwamared Aminu Gwarzo, tsohon mataimakin gwamnan Kano shi me dan takarar da ke tare da jagoran Kwankwasiyya kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Jerin sunayen yan takarar gwamnan Kano ya ƙunshi Gashash Mukhtar na jam’iyyar AP, Haruna Abdullahi na AA, Sharif Abba na AAC, Ibrahim Ali Amin na ADC da Muhammad Abdullahi na ADP.
Sauran ’yan takarar sun haɗa da Yusuf Abba Kabir na APC, Tijjani Sukairaju Tijjani na APGA, Muhammad Bashir Galadanchi na APM, Tukur Aliyu Malam na APP, Ahmad Furera na BP da Bari Mustapha Bello na DLA.
Karin bayani na nan tafe....
Asali: Legit.ng
