Tinubu Must Go: Yan Sanda Sun Faɗi Abin da Faru bayan Zargin Hana Masu Gangami
- Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yi magana kan dalilin da ya sa jami’ansa suka tare wurin taron masu adawa da Shugaba Tinubu a Kano
- Bakori ya ce ’yan kungiyar Tinubu Must Go suna da ’yancin gudanar da taronsu, amma sanar da ’yan sanda zai taimaka wajen tabbatar da tsaronsu
- Kwamishinan ya ce sun dauki matakin ne saboda fargabar barazanar tsaro, musamman bayan cafke wasu mutane da makamai a Sabon Gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya yi martani kan zargin hana shirya taron kungiyar Tinubu Must Go (TMG) a Kano.
Bakori ya ce rundunar ta damu kwarai da tsaron mambobin kungiyar da mazauna jihar wanda aka samu matsala yayin gangamin.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu mambobin kungiyar TMG sun nuna rashin amincewarsu da matakin ’yan sanda a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take
Abin da Abba Hikima ke zargi
A wani bidiyo kai tsaye da ya wallafa, Abba Hikima, daya daga cikin wadanda suka shirya taron, ya yi zargin cewa an jibge motocin ’yan sandan kwantar da tarzoma kusan 10 a wurin da za a gudanar da taron.
Ya ce matakin ya saba wa ’yancinsu na kasa a matsayin ’yan Najeriya, yana mai jaddada cewa doka ba ta bukatar su nemi izini kafin shirya taronsu.
Hikima ya ce:
“Kuna iya gani cewa an riga an jibge motocin ’yan sandan kwantar da tarzoma sama da 10 a nan.
“An ajiye motocin ne domin hana mu shiga wani wurin taro mai zaman kansa da muka biya kudi domin amfani da shi. Mun shirya taruwa ne domin amfani da ’yancinmu na kasa. Wannan shi ne ma karin dalilin da ya sa dole Tinubu ya tafi."

Source: Facebook
Abin da kwamishinan yan sanda ya ce
Sai dai da yake mayar da martani kan lamarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, Bakori, ya amince cewa mambobin TMG suna da ’yancin gudanar da taronsu.

Kara karanta wannan
Kwamishinan 'yan sandan Kano ya yaba wa Sarki Aminu Ado kan muhimmin abin da ya yi
Ya ce, duk da haka, yana da muhimmanci su sanar da rundunar domin ta kare su tare da hana duk wata barazana ga zaman lafiyar jihar.
Bakori ya ce:
“Abin da ya faru shi ne, da farko, hakkinsu ne su zo su shirya taronsu. Babu wanda zai hana su, kuma doka ba ta bukatar su sanar da mu.
“Amma sanar da mu yana da muhimmanci domin zai ba mu damar tsara yadda za a gudanar da taron, tabbatar da cewa babu tashin hankali, babu wanda zai kai musu hari, kuma ba za su aikata wani abu a Kano da zai zama laifi ba.”
Ya ce a daren da ya gabata, ya ga a kafafen sada zumunta cewa suna shirin gudanar da taro, saboda haka, ya kira Lauya Hikima ta waya domin jin abin da ke faruwa.
Kwamishinan ya ce idan mutane 700 za su shigo Kano, wajibi ne rundunar ta san cikakkun bayanansu.
!Ya bayyana cewa wannan ba shi ne karon farko da kungiyoyin siyasa daga jam’iyyu daban-daban suke shirya ayyukansu a jihar ba.
Ya ce irin wadannan kungiyoyi sukan rubuta wa rundunar wasika, sannan ’yan sanda su samar musu da tsaro.
Bakori ya ce ya bukaci Hikima ya dage taron, sannan ya zo ofishinsa domin su tattauna lamarin.
A cewarsa, Hikima ya ce zai tuntubi sauran masu shirya taron, sannan ya dawo da amsa. Sai dai kwamishinan ya ce ya kira shi sau da dama daga baya, amma bai amsa wayarsa ba.
An ba da belin yan Tinubu Must Go
Mun ba ku labarin cewa wata kotun majistare a Maiduguri ta bayar da belin mutane biyar da aka kama bisa zargin adawa da Bola Tinubu.
Yan sanda sun ce sun kama mutanen da wasu kayayyakin da ake zargin tabar wiwi, ƙwayoyin D5 da tukunyar shisha.
Lauyan masu shari’ar ya tabbatar da sakin mutanen, tare da kira ga matasa su kiyaye doka yayin amfani neman ’yancinsu.
Asali: Legit.ng
