Abokin Takarar Atiku, Amaechi Ya Haukatar da Magoya Bayan shugaba Tinubu

Abokin Takarar Atiku, Amaechi Ya Haukatar da Magoya Bayan shugaba Tinubu

  • Rotimi Amaechi yana da ra’ayin cewa kuri’un Bola Tinubu suna wajen barayi da mahaukata a Najeriya
  • ‘Dan takaran mataimakin shugaban kasar na jam'iyyar ADC ya ce mahaukaci ne zai zabi APC a takarar 2027
  • Amaechi ya ce idan aka ga gwamnatin Tinubu tana aiki, kudin da za ta samu take hari ba cigaban jama’a ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Edo - Rotimi C. Amaechi mai neman takarar mataimakin shugaban kasa a ADC ya ragargaji magoya bayan jam'iyyar APC.

‘Dan takaran yana ganin babu wani mutumi mai hankali da zai kada kuri’arsa ga jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027.

Rotimi Amaechi
Rotimi Amaechi da Hadi Sirika lokacin suna ministoci a gwamnatin Muhammadu Buhari Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rotimi Amaechi ya kai kamfen ADC zuwa Edo

Rotimi Amaechi ya yi kira ga mutanen jihar Edo su kaurace wa zaben Bola Tinubu kamar yadda The Cable ta rahoto.

A babban zaben da za a yi a shekarar badi, Amaechi yana so mutanen jihar su goyi bayan jam’iyyarsu ta ADC mai adawa.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Tunanin Tinubu ya mamaye zuciyar minista, yana zuwa har a cikin barci

Amaechi yake cewa barayi ne kurum za su goyi bayan takarar Tinubu a 2027 sai kuma mutanen da ba su da hankali.

"Suna zuwa suna cewa ‘A zabi Tinubu!’ A zabi Tinubu! Barayi ne kadai za su iya zaben Tinubu.
"Kai, na ga maganar wani a dandalin sada zumunta yana cewa ‘A 2027 ne za mu san mahaukata nawa mu ke da su a Najeriya.
“Domin mahaukata ne kurum za su zabi Tinubu. Idan mutanen Edo suka zabi Tinubu, hakan yana nufin mutanen Edo mahaukata ne. Idan ku ba mahaukata ba ne, Tinubu ba zai ci zabe a nan ba.”

- Rotimi Amaechi

'Dan takaran ADC ya soki ayyukan Tinubu

Daily Trust ta ce Amaechi ya zargi gwamnatin Tinubu da yin ayyuka saboda kudin da za su samu ba don amfanin jama’a ba.

Tsohon ministan ya soki kokarin gina wata sabuwar tashar ruwa da ake yi a Ogun, ya ce jihar ba ta bukatar wannan namijin aiki.

Kafin shigarsa ADC a bara, Amaechi ya yi shekaru kusan 12 a jam'iyyar APC tun da ya bar PDP a 2013.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi wa APC tonon asiri, ya ce ta kawo sabuwar dabara a 2027

Amaechi zai hada mutane fada da Tinubu

Ya kuma fada wa mutane cewa Tinubu bai son su, yana kashe kudi wajen kwangiloli ne saboda abin da zai shigo masa.

"Saboda haka Tinubu ya tsane ku. A’a, ba wasa na ke yi ba. Idan da Tinubu bai tsane ku ba, me zai sa ya gina wani karin tashar ruwa?"
"A Ogun wasu kaya ake samarwa? Wasu kaya mu ke samarwa da za mu bukaci wadannan tashohi? Ba saboda yana son mutanen Ogun ba ne. Kudin da zai samu daga aikin ne."

Shugabannin ADC sun je suna fada

An ji labari cewa Dr. Bamidele Ekundayo mai shekaru fiye da 70 ya yi fada da Ilesanmi Omolayo saboda siyasa da neman shugabancin ADC.

A kan rikicin neman shugabancin jam’iyya ne jami’an tsaro suka watsa su a wani karamin kotun majistare da ke garin Ado Ekiti a jihar Ekiti.

Bayan an sha turanci a gaban alkali, lauya ya karbo belin manyan ‘ya ‘yan na ADC a Ekiti a kan N100,000 tare da kawo wani ya tsaya masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng