Mutuwar Uwar Amaechi: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Fusata kan Siyasantar da Batun

Mutuwar Uwar Amaechi: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Fusata kan Siyasantar da Batun

  • Hadimin shugaban kasa ya soki Rotimi Amaechi kan cewa manufofin tattalin arzikin Bola Tinubu sun haddasa rasuwar mahaifiyarsa
  • Mai ba Shugaba Tinubu shawara kan sadarwa da manufofi ya zargi Amaechi da yada labaran karya da kalaman siyasa masu neman jawo hankalin jama’a
  • Ya ce har mutumin da ke ba Peter Obi shawara ba zai yarda cewa manufofin Tinubu ne suka kashe mahaifiyar Amaechi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan sadarwa, Daniel Bwala, ya yi magana game da sukar manufofin shugaban kasa da ake yi.

Bwala ya yi wa tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, ba’a da ya ce manufofin Tinubu ne suka haddasa rasuwar mahaifiyarsa.

Amaechi ya sha suka daga Fadar shugaban ƙasa
Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi. Hoto: Rt. Hon. Rotimi Chibuike Amaechi.
Source: Twitter

Bwala ya yi wannan kalamin ne ranar Laraba, yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Labaran bogi da suka rika yawo a kafafen sada zumunta a makonnin nan

Ya zargi Amaechi da yada abin da ya kira labaran karya da kalaman neman farin jini gabanin zaben shugaban kasa na 2027 mai zuwa.

Kalaman Amaechi da suka jawo maganganu

Amaechi, wanda shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ADC, ya yi wannan kalami mai cike da ce-ce-ku-ce yayin wata hira da talabijin.

An tambaye shi ko manufofin tattalin arzikin Shugaba Tinubu ne suka haddasa rasuwar mahaifiyarsa, inda ya amsa cikin raha da cewa mahaifiyarsa tana cikin koshin lafiya kafin Tinubu.

Ya ce:

“Tabbas, kafin Tinubu, mahaifiyata tana cikin koshin lafiya."
Hadimin Tinubu ya caccaki Amaechi kan siyasantar da mutuwar mahaifiyarsa
Shugaba Bola Tinubu da Rotimi Amaechi. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Martanin Bwala kan kalaman Amaechi

Sai dai Bwala ya yi amfani da wannan kalami wajen mayar da martani ga hare-haren da Amaechi ke kai wa gwamnatin Tinubu a baya-bayan nan

Bwala ya ce ya taba aiki a bangaren Atiku kuma ya ga abin da Amaechi ke kawowa bangaren, yana ganin yana kawo abin da za a kira shirme.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu da abokinsa suka kusa fada wa gadar Legas a hadarin mota

Bwala ya ware batun mahaifiyar Rotimi Amaechi a matsayin daya daga cikin misalan abin da ya kira kalaman karya da tsohon gwamnan ya yada

Ya ce:

“Amma yana kuma kawo labaran karya, salon siyasar neman farin jini, maganganu marasa tushe da kuma kalaman karya.
“Daya daga cikin kalaman karya da ya yada shi ne cewa manufofin tattalin arzikin Shugaban kasa sun kashe mahaifiyarsa."

Daga nan Bwala ya janyo Peter Obi cikin martanin nasa, inda ya ambaci wani kalami mai cike da ce-ce-ku-ce da aka taba alakanta shi da dan takarar shugaban kasa na NDC.

“Ko mahaukacin da ya kasance yana ba Peter Obi shawara ba zai yarda cewa manufar tattalin arzikin Shugaba Tinubu ta kashe mahaifiyar Amaechi ba."

- In ji Bwala

Wannan takaddama ta kara nuna yadda yakin kalamai ke kara tsananta tsakanin gwamnatin Tinubu da ‘yan adawa yayin da yakin neman zaben 2027 ke kara karfi

'Abin da za mu fara yi a gwamnati' - Amaechi

Mun ba ku labarin cewa Rotimi Amaechi ya yi alkawarin rage tsadar sufuri, man fetur da abinci idan suka lashe zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

"Yan Najeriya ba su cancanci haka ba," Atiku ya sake aika sako mai ɗaga hankali ga Tinubu

Ya ce gwamnatin da za su kafa za ta mayar da hankali kan farfado da tattalin arziki da rage tsadar rayuwa.

Yan adawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 musamman ADC sun yi alkawarin cewa za su dawo da tallafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.