Rikicin na Hannun Daman Tinubu da Gwamna Radda Ya Kara Daukar Zafi
- 'Yan sanda sun sake gayyatar jami’an tsaron Gwamna Dikko Radda, SP Abdulganiyu da DSP Hassan Bello, domin yi musu tambayoyi kan lamarin da ya shafi fastocin yakin neman zaɓe
- Wasu majiyoyi sun ce an gayyaci jami’an tsaron ne kawai, yayin da wasu suka ce shugaban ma’aikatan gwamnan, Abdulkadir Mamman Nasir, ma yana cikin waɗanda aka kira
- Rikicin ya samo asali ne daga zargin lalata allunan tallan kamfen da ke ɗauke da hoton Shugaba Bola Tinubu, lamarin da ya haddasa rarrabuwar kawuna a APC ta jihar Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Akwai alamun rikicin siyasa tsakanin Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, da mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa da sauran batutuwa, Malam Ibrahim Kabir Masari, ya sake daukar sabon salo.
Hakan ya biyo bayan sake gayyatar jami’an tsaron gwamnan guda biyu da ’yan sanda suka yi, ciki har da babban jami’in tsaronsa (CSO), SP Abdulganiyu, da mai gadinsa (ADC), DSP Hassan Bello.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce wasu majiyoyi sun ce jami’an tsaron biyu ne kawai aka gayyata, yayin da wasu suka bayyana cewa shugaban ma’aikatan gwamnan, Abdulkadir Mamman Nasir, ma yana cikin waɗanda aka kira domin yi musu tambayoyi.
Rahotanni sun nuna cewa ba a sake ganin jami’an tsaron a bainar jama’a a Katsina ba tun ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026.
Wata majiya a gidan gwamnatin jihar da ta yi magana da jaridar a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamban 2027 bisa sharaɗin ɓoye sunanta, ta tabbatar da cewa an gayyaci jami’an, kuma ana tsare da su dangane da batun fastocin kamfen.
Gwamnatin Radda ta yi magana kan gayyatar
Da aka tuntubi Darakta Janar na yaɗa labaran gwamnan, Maiwada Danmalam, domin jin ta bakinsa kan sake gayyatar jami’an tsaron, ya ƙi yin tsokaci.
Ya ce ba shi da izinin yin magana a madadinsu, amma ya musanta rahotannin cewa an kama shugaban ma’aikatan gwamnan.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu
Danmalam ya ce:
“Rahoton cewa an kama shugaban ma’aikata ba gaskiya ba ne. Ina tare da shi a wannan yammacin.”
Ya bayyana cewa Nasir yana gudanar da wasu ayyukan ofis ne a ofishin kamfen na Tinubu da Dikko na shiyyar Katsina APC da ke Dandagoro, Batagarawa.
An gano cewa hedikwatar rundunar ’yan sanda ta ƙasa da ke Abuja ce ta sake gayyatar jami’an tsaron a farkon makon nan. Tun daga lokacin ba a sake ganin su a bainar jama’a ba.
Wannan lamari ya haifar da tambayoyi kan ko ’yan sanda sun sake buɗe binciken da suka gudanar a baya game da lalata allunan tallan kamfen, ko kuma suna binciken wasu sabbin zarge-zarge.
Rikicin ya samo asali daga lalata allunan kamfen
Sabuwar gayyatar ta sake tayar da muhawarar da ta fara watannin baya, bayan zargin lalata allunan tallan kamfen da ke ɗauke da hotunan Shugaba Tinubu.
Lamarin ya zama tushen saɓani tsakanin ɓangaren siyasar Radda da wata ƙungiyar ’yan siyasa da ke Abuja, wadda ake alaƙantawa da Masari.
Ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga rundunar ’yan sanda kan sake gayyatar jami’an biyu bai yi nasara ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Katsina, DSP Sadik Aliyu, bai amsa kiran waya da saƙonnin tes da aka aika masa ba kafin kammala haɗa rahoton.
Yadda saɓanin Radda da Masari ya fara bayyana
Saɓanin da ke tsakanin Radda da Ibrahim Masari ya daɗe yana gudana ne a ɓoye, har sai da aka kama mai gadin gwamnan da babban jami’in tsaronsa a watan Agusta dangane da zargin lalata allunan tallan kamfen.
Rikicin ya kuma haifar da rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Katsina. An samu ɓangarori biyu da ake kira “Katsina APC” da “Katsina/Abuja APC”.
Na farko ya ƙunshi mambobin APC da ke zaune a jihar, waɗanda ake ganin suna biyayya ga Gwamna Radda.
Na biyun kuma ya ƙunshi ’yan siyasar Katsina da ke riƙe da manyan muƙamai a gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
Sai dai Maiwada Danmalam, Darakta Janar na yaɗa labaran gwamnan, ya taɓa musanta sanin wani rikicin siyasa tsakanin Radda da Masari.
A baya, ya bayyana cewa:
"Ban san wani rikicin siyasa da ke tsakanin gwamnan da Malam Kabir Ibrahim Masari ba. A gaskiya, a yanzu ne na fara jin wannan batu daga gare ku.”
Radda ya faranta ran sarakuna
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayar da umarnin gaggauta biyan duk haƙƙoƙin kuɗi da ake bin sarakunan gargajiya a faɗin jihar.
Ya kuma buƙaci sarakunan da ke fuskantar jinkirin biyan haƙƙoƙinsu da su kai ƙorafinsu kai tsaye ofishinsa, tare da gabatar da cikakkun bayanai domin ɗaukar matakin gaggawa.
Asali: Legit.ng


