‘Amaechi Ya Fifita Garin Buhari fiye da na Shi, Za Mu Koya Masa Hankali’: Wike
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya zargi tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da yin watsi da matsalolin Rivers
- Wike ya ce Amaechi ya taimaka wajen kai Jami’ar Sufuri ta Tarayya Daura, mahaifar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari
- Ministan ya ce Bola Tinubu ya cancanci a kira shi “ɗan’uwa” ga mutanen Rivers saboda ya fahimci matsalolinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon gwamnan Rivers kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC a 2027, Rotimi Amaechi.
Wike ya zargi Amaechi da yin watsi da jiharsu ta Rivers inda ya fifita wasu garuruwa fiye da na shi a gwamnatocin baya.

Source: Facebook
Wike ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin wata liyafar girmamawa da aka shirya masa a Omagwa, ƙaramar hukumar Ikwerre da ke Rivers, cewar TheCable.
Wike na zargin Amaechi da rashin katabus
Da yake jawabi a wajen taron, Wike ya ce Amaechi bai magance matsalolin Rivers ba a lokacin da yake Ministan Sufuri na Tarayya.
Ministan ya kuma zargi Amaechi da taimakawa wajen kafa Jami’ar Sufuri ta Tarayya a Daura, Katsina, mahaifar marigayi Shugaba Buhari.
Wike ya ce Amaechi ya ɗauki wannan mataki ne saboda yana ganin hakan zai taimaka masa wajen cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.
Ya ce:
“Yanzu da yake son neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa, dole mu tambaya: me ya faru a duk shekarun da ya kasance Ministan Sufuri?
“Shin ya yi hulɗa da mu? Shin ya yi tunanin matsalolinmu? Shin ya kawo wani abu nan?, maimakon haka, kun kai jami’a Daura saboda kuna tunanin hakan zai sa ku zama shugaban ƙasa. Shin hakan ya sa kuka zama shugaban ƙasa?”

Source: Twitter
‘Tinubu ɗan’uwanmu ne’
Wike ya ce a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Amaechi ya bayyana ma’anar ɗan’uwa ba wai wanda suke da jini ɗaya ba ne kawai.
A cewar Wike, Amaechi ya ce ɗan’uwa shi ne mutumin da yake tsayawa tare da wasu a lokacin ƙalubale kuma ya fahimci matsalolinsu, cewar Punch.
Ya ce Amaechi ya taɓa cewa Jonathan ba za a ɗauke shi a matsayin “ɗan’uwa” ga mutanen Rivers ba, yayin da ya nemi mazauna jihar su ɗauki Buhari a matsayin ɗan’uwansu.
Wike ya yi amfani da wannan ma’ana da Amaechi ya bayar wajen cewa tsohon ministan ba zai iya zama ɗan’uwa ga mutanen Rivers ba saboda ya yi watsi da su.
Ministan Abuja ya ce Shugaba Bola Tinubu ya yi abubuwan da suka sa ya cancanci a ɗauke shi a matsayin “ɗan’uwa” ga mutanen Rivers.
Wike ya ce, “Ya ce ɗan’uwa shi ne wanda yake tare da kai a lokacin wahala, yake hulɗa da kai, kuma yake tunanin jin daɗinka da rayuwarka.”
Ya ƙara da cewa:
“A cewarsa, ɗan’uwa ba wai batun jini ba ne, batun rayuwa da ci gaba ne.”
Wike ya ce, “Lokacin da Jonathan yake shugaban ƙasa, ɗan’uwanmu Amaechi ya ce Jonathan bai taɓa kula da mu ba, saboda haka ba zai iya zama ɗan’uwanmu ba.

Kara karanta wannan
Tsakanin Atiku da Obi waye zai iya ƙalubalantar Tinubu? an fadi wanda ya zo da gaske
“Ya gaya mana cewa Muhammadu Buhari ɗan’uwanmu ne saboda Buhari zai tsaya tare da mu kuma ya yi hulɗa da mu.”
Wike ya ce Amaechi bai da tasirin siyasa
A baya, an ji cewa Ministan Abuja Nyesom Wike ya yi magana game da tasirin siyasar dan takarar mataimakin shugaban kasa, Rotimi Amaechi.
Wike ya zargi Amaechi da sauya matsaya kan zaben fidda gwani na APC, yana cewa yanzu yana cin moriyar tsarin da ya taba suka.
Ministan ya yabawa gwamnatin Tinubu kan ayyukan ci gaba a Ribas, yana cewa jihar ta samu kulawar tarayya fiye da lokutan baya.
Asali: Legit.ng

